Ogun ta maya gurbin Likitocin dake yajin aiki da likitocin sa kai

0

Gwamnatin jihar Ogun ta maya gurbin Likitocin dake yajin aiki dake aikin kula da masu fama da cutar Korona a asibitin Olabisi Onabanjo dake jihar da likitocin sa kai.

Idan ba a manta ba a ranar 1 ga watan Yuli ne Likitocin kungiyar ARD ta fara yajin aiki a dalilin rashin biyan bukatun su da gwamnati ta ki yi.

Wadannan bukatu kuwa sun hada da rashin samar wa ma’aikatan kiwon lafiya inshoran lafiya, rashin biyan ma’aikatan lafiya da sabon tsarin biyan albashin ma’aikata, rashin isassun ma’aikata, rashin biyan alawus da sauran su.

Kungiyar ARD ta ce rashin biyan bukatun su da gwamnati ta ki yi duk da barazanar da ta rika yi na zuwa yajin aiki, sannan gwamnati tayi burus da su ya nuna bata shirya neman ayi sulhu ba.

Mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yada labarai Olabisi Onabanjo ya tabbatar da haka yana mai cewa gwamnati ta yi haka ne domin ci gaba da aiyukan kula da masu fama da cutar covid-19 a asibitin.

“Tabas ma’aikatan lafiya na da damar yin
yajin aiki amma gwamnati zata tattauna da su domin a warware matsalar.

Sakataren kungiyar ARD Kuma sakataren asibitin Olabisi Onabanjo OOUTH, Tope Osundara a hira da yayi da jaridar Punch ya ce na sa ran za a sasanta a cikin wanna mako.

Yanzu mutum 1,174 ne suka kamu da cutar a jihar Ogun.

Daga ciki 302 na kwance a asibiti, an sallami 850 sannan 20 sun mutu.

Share.

game da Author