Idan ka za a tambayi masu fashin-bakin siyasa da sauran ‘yan Najeriya dangane da salon mulkin Buhari, to cewa za su rika yi da dadi, ba dadi da kuma tsananin kunci.
Sai dai kuma daga cikin bangaren da za a fi ganin laifin sa, akwai dabi’ar lusarancin da ya ke nunawa, wajen kin maida kai ya yayyafa wa wutar rikicin siyasa ruwa da ke yawan tirnike jam’iyyar sa, APC.
Tun bayan hawan sa APC ta afka cikin kwazazzabon rikice-rikice, amma Buhari ba ya maida hankali, har sai bayan ruwa ya ci jam’iyyar sannan ko dai ya yi fargar-Jaji ko kuma ya ceto jam’iyyar bayan ta galabaita.
Rikicin da ya yi sanadiyyar sauke Adams Oshiomhole dadadde ne, amma Buhari bai taba kokarin sasantawa ba. Har abin ya yi munin da Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya fice daga APC zuwa PDP.
‘Hali Zanen Dutse’:
Yayin da wasu ke ganin cewa Buhari bai damu da ganin APC ta dore bayan kammala wa’adin sa na zango na biyu ba. Wasu kuma cewa suke yi dama can halin sa ne, idan aka yi la’akari da yadda kashe-kashe ke kamari a kasar nan, kuma ya ki canja Shugabannin Tsaron Kasa, duk kuwa da kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya ke yi a tsige su.
Shi kuma Kakakin Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina, kare Buhari ya yi, ya ce Buhari ya fi so dimokradiyya ta rika aikin ta, maimakon ya rika yi wa dimokradiyya katsalandan.
Tun Ranar Gini Tun Ranar Zane:
Da dama na ganin cewa irin wannan lusaranci da Buhari ke nunawa wajen kin maida hankali ga dinke babbar barakar jam’iyya, shine ya kashe jam’iyyar CPC ta kaca-kaca.
Irin yadda CPC ta yamutse kuma ta dagule, hakan na ci gaba da faruwa a cikin APC, tun a cikin shekara ta 2015, bayan Buhari ya hau mulki.
Asarar APC A Jihohin Rivers Da Zamfara:
Buhari na ji ya na gani ana shirya tuggun kwatagwangwamar harkallar zaben fidda-gwani da na shugabancin jam’iyya a jihohin Rivers da Zamfara. Amma bai yi magana ba. Har sai da abu ya rincabe, ya kazamce, aka rika luguden shari’u a kotuna daban-daban.
A Jihar Rivers Minista Rotimi Amaechi da ‘yan APC bangaren sa, sun gudanar da zabukan fidda-gwani, tare da tsaida na hannun damar Amaechi takarar Gwamna.
Bangaren Sanata Magnus Abbey sun kai kara kotu, a karshe kotu ta ce zaben-fidda-gwanin APC na Jihar Rivers haramtacce ne, domin reshen Magnus Abbey ba a ba su damar shiga zaben ba. Karshe dai APC ko zaben ba a bari ta shiga ba.
Ibtila’in da ya afka wa APC a Rivers, irin sa ne ya afka wa jam’iyyar a Jihar Zamfara. Duk kasar nan kowa ya ga irin yadda tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari ya shafe shekaru ya na rikici da Sanata Marafa, har sai da APC ta gurgunce a Zamfara, amma Buhari bai sa baki ya ja kunnen Yari ba. A karshe Kotun Koli ta hana APC ko da kujerar kansila ce balle ta gwamna.
Yadda Bola Tinubu Da Oyegun Suka Rika Keta Wa Juna Riga A Gaban Buhari:
Manyan dattawan APC biyu, wato jigon jam’iyyar, Bola Tinubu da kuma shugaban jam’iyya na kasa na lokacin, Odige Oyegun sun koma ‘yan-yaga-riga a gaban Buhari, suka rika kek-keta wa juna rigar mutunci tun a cikin 2016.
Wannan rikici ya dabaibaibaye jam’iyyar har ta kai an nemi kai ruwa rana a gaban Buhari a yayin taron masu ruwa da tsaki na APC.
Asalin sabanin shi ne Tinubu ya zargi Oyegun da yin azarbabin damka sunan Rotimi Akeredolu a matsayin Dan takarar fidda-gwanin da APC ta tsayar da zaben gwamnan Ondo, cikin 2016.
Daga karshe dai su biyun sun rika yi wa juna kaca-kaca a kafafen yada labarai, tare da amfani da muggan kalmomi suna jifar juna da su
Ra’ayoyin Masana Siyasa Dangane Da Irin Salon Ko-in-kula Din Buhari:
Masana siyasa daban-daban sun yi wa PREMIUM TIMES karin bayani, fashin-baki da kuma yi wa jaridar fassarar game-gari a kan yanayin Buhari.
Sai dai wanda ya fi daukar hankali, shi ne bayanin da wani dan gwagwarmayar dimokradiyya mai suna Inibehe Effiong.
Cewa ya yi irin yadda Buhari ke nuna ko-in-kula kan matsalolin APC, ya na nuna bai damu ba, to irin haka ya ke rike da akalar Najeriya.
“Shin tun farko ma ku duba ku gani mana. Sai da Buhari ya shafe watanni shida a mulki kafin ya nada ministoci. Sannan ya shafe shekaru bai nada shugabanni da mambobin hukumomin ma’aikatun gwamnati ba. To irin yadda ya ke yi wa mulkin Najeriya tafiyar-hawainiya, haka ya ke wa jam’iyyar APC.”
Ra’ayin Effiong ya zo daidai da na masu cewa, “shi fa Buhari kan sa kadai ya sani. Tunda dai ya haye kujerar mulki, to bai damu da dorewar jam’iyya ko nasarar wani ba. Kowa ta sa ta fisshe shi kawai.”