Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa NAPTIP reshen jihar Kano ta cafke masu safaran mutane guda uku sannan sun ceto mutum 71 daga hannun su a jihar.
Kwamandar hukumar na shiyar jihar Kano Shehu Umar ya sanar da haka ranar Juma’a da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.
Ya ce hukumar ta yi wa masu safaran mutane diran mikiya bayan ta samu bayanan siri kan aiyyukan safarar mutane a jihar.
“A dalilin haka ne hukumar ta farautar wadannan mutane daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Yuli inda har aka yi nasarar damke su.
“Daga cikin mutum ukun da muka damke mutum biyu ‘yan kasar Kamaru ne daya dan Najeriya sannan shekarun su duka ba su wuce 21 zuwa 36 ba.
“An Kama wadannan mutane yayin da suke hanyar zuwa kasashen Algeria, Morocco da Libya.
Bayan haka Mutum 18 daga cikin mutum 71 din da za a yi safarar su daga kasar Kamaru suke inda daga ciki akwai maza 14, Mata 4.
Sauran mutane 19 da suka rage daga Najeriya suke, maza 11, Mata 8 duk kuma ‘yan daga jihar Kano.
Umar ya ce za a damka mutum 18 ga gwamnatin kasar Kamaru domin ci gaba da bincike.
Ya Kuma ce hukumar ta karbi Mutum 34 da hukumar NIS ta ceto a jihar Katsina.
“An Kama wadannan mutane ba tare da cikakkun takardun tafiya ba sannan ga dukkan alamu a hanyar su na kokarin ficewa daga kasar nan.