Najeriya ta karbi tallafin dala miliyan 890 don yaki da cututtuka daga ‘Global Fund’

0

Asusun bada tallafi na duniya ‘Global Fund’ ta tallafa wa gwamnatin Najeriya da dala miliyan 890 domin yaki da cututtuka a kasar.

Wadannan cututtuka sun hada da cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro da tarin fuka.

Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya Sanar da haka a makon da ya gabata a Abuja.

Ehanire ya ce samun wannan tallafi zai taimaka wajen inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan musamman bangaren yaki da wadannan cututtuka da suka yi wa kasar nan katutu.

Idan ba a manta ba a watan Janairu 2020 Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta ciwo bashin dala miliyan 890 daga asusun duniya domin dakile yaduwar cututtuka a kasar nan.

Gwamnati ta ce za ta kashe wadannan kudade wajen yaki da cutar Kanjamau, Zazzabin Cizon Sauro da tarin fuka daga shekarar 2021 zuwa 2023.

Gwamnati ta ce yaki da zazzabin Cizon Sauro ne zai samu kaso mafi tsoka daga cikin wadannan kudade da ya kai dala miliyan 417, Kanjamau dala miliyan 329 sannan tarin fuka dala miliyan 143.

Ya kara da cewa gwamnati ta tsara matakan da za su taimaka mata wajen yadda kashe wadannan kudade yadda ya kamata ba tare da wani ko wasu sun yi sama da fadi da su ba.

Share.

game da Author