Naira bilyan 3.4 aka dagargaje a Hukumar NSITF, shi ya sa aka dakatar da shugaba da daraktocin ta – Gwamnati

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa an bi dukkan ka’idoji da sharuddan da doka ta tanadar wajen dakatar da Shugaba, wato Babban Daraktan Hukumar Zuba Jarin Inshorar Ma’aikata (NISTF) da wasu daraktocin hukumar.

Wannan bayani ya fito ne bayan wani reshe na Kungiyar Kwadago ya zargi gwamnati cewa ba ta bi ka’idojin da suka dace ba wajen dakatar da manyan mahukuntan na NSITF.

A kan haka ne Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Kwadago, Charles Akpan ya fitar da sanarwa cewa tabbas gwamnati ta bi duk wata hanyar da ta dace sannan ta dakatar da su.

Akpan ya ce don haka Ministan Harkokin Kwadago, Chris Ingige ya bi tsarin da doka ta tanadar sannan ya dakatar da su.

“Daga cikin dalilan dakatar da su din akwai yadda suka dagargaje naira bilyan 3.4, aka rika kirkiro kwangilar kakuduba domin a rika karkatar da kudaden.

“Sai suka karkatsa kwangilolin har gida 196, don kada a rika buga tandar neman ‘yan kwangila, suka rika raba aikin su-ya-su.

“Tuni har sun cire naira bilyan 2.3 a matsayin kudaden biyan kwangilolin da kwata-kwata babu su kuma babu alamun su. Sun kuma fatattaka kudaden a tsakanin su.

“Saura naira bilyan 1.1, wato cikon naira bilyan 3.4 kuwa su suke jira gwamnati ta sakar musu, su danne su kwashe, su zuba aljifan su.” Inji Akpan.

Ya ce sun kuma yi cuwa-cuwar aikin gina ofisoshin shiyya har 14 na kasar nan. Suka yi wa kwangilar rabon-naman-kuraye, kudin da sun kai bilyoyin nairori.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda aka dakatar da su, har aka nada jagorori na riko, wadanda za su fara aiki ranar Litinin, 6 Ga Yuli.

Cikin wadanda aka dakatar har da Jesper Azutalem, babban daraktan hada-hadar kudade.

Jama’a sun yi mamakin ganin sunan Jesper cikin sunayen rundunar kamfen din zaben gwamnan Edo da APC ta kafa, duk kuwa da cewa akwai sunan sa cikin wadanda aka dakatar.

Share.

game da Author