Darektan yada labarai na ma’aikatan jinkai, Rhoda Iliya, ta bayyana cewa akalla mutum sama da milyan 5 ne suka cika fom din neman aikin N-Power a Najeriya zuwa yanzu.
Tun da farko dai hukumar ta bayyana cewa guraban da aka ware na mutum 400,000 ne kacal amma kuma zuwa yanzu man samu matasa sama da Milyan 5 da suka cika Fom din neman aikin N-Power din.
Sai dai kuma duk da samun dandazon masu neman aikin, hukumar ta kara makonni biyu domin wadanda suka samu matsala wajen cika Fom din a farkon bude shafin su samu su cika.
Idan ba a manta ba kwanakin baya jaridar Saharareporters ta wallafa cewa ministan ma’aikatar jinkai, Sadiya Farouq ta raba wa yan mjajalisa gurabe 50,000.
Daga baya shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya karyata wannan zargi inda ya ce babu wani abu mai kama da haka da ya auku tsakanin majalisar da minista Sadiyya.
Haka kuma, wadanda suka kammala shirin na A da B, sun gudanar da zanga-zanga a makon jiya suna kira ga hukumar su biya su kudaden alawus dinsu na na watanni uku da ba a biya su ba.
Matasan sun garzaya har majalisar Kasa domin mika kukan su ga majalisar.
Bayan wannan zanga-zanga, minista Sadiyya ta bayyana cewa an gano harkalla mai dinbin yawa ne a shirin da dole sai anyi tankade da rairaya kafin a biya sauran kudadedn watannin da ba a biya matasan ba.