An kiyasta cewa an kashe mutum 2,732 a Najeriya cikinwatanni biyu kacal, daga Afrilu zuwa Yuni.
Rahoton wadda cibiya mai suna SBM intelligence ta fitar a Lagos, ta ce ta tattara bayanan ne a daga rahotannin da jsridu daban-daban ke wallafawa a kasar nan.
Rahoton ya tattara kididdiga daga jaridu da suka hada da kashe-kashen gilla, sun hada da kisa daga Boko Haram, kisa a bangaren masu garkuwa da mutane, samamen ‘yan bindiga, hare-haren makiyaya da kuma kashe-kashen da ke da kusanci da kabilanci da yankunan karkara.
Wannan gagarimin aikin kididdiga na hadin-gwiwa ne tsakanin cibiyar SBM Intelligence da kuma wata kungiya mai suna ‘Enough is Enough”
Cikin watan Afrilu dai SBM ta wallafa kididdigar kisan-gilla ga kusan mutum 1,000 da ce su ne adadin wadanda jaridu suka buga an yi wa kisan-gilla tsakanin watan Janairu zuwa Maris, 2020.
SBM ta ce rahoton ya jibinci hujjoji daga bangarorin nazarin harkokin tsaro, kungiyoyi masu sa-ido kan tabarbarewar matsalar tsaro na waje da kuma na cikin gida. Kuma duk ta lissafa sunayen kungiyoyin.
“Kisan-gilla kan wadanda ba su ji ba, kuma ba su gani ba ya kara tsananin muni saboda rashin maida hankali kacokan da gwamnati da jamii tsaro suka yi wajen kokarin dakile kashe-kashen.”
Rahoton ya kuma yi tsokacin yadda kulle jama’a gida saboda cutar Coronavirus ya haifar da kuncin rayuwa da rashin aikin yi ga matasan da aka yi kiyasi kusan kashi 43%.
Daga daga cikin masu nazarin harkokin tsaro a SBM Intelligence, mai suna Confidence Isaiah, ya bayyana wasu dalilan da suka haifar da karuwsr kashe-kashen tsaanin Afrilu zuwa Yuni.
Isaiah ya ce akwai kisan-gillar da Boko Haram suka rika yi wa sojoji, Sannan kuma ‘yan bindiga sun rikide daga satsr shanu da garkuwa da mutane, sun koma amfani da zabga-zabgan makamai su na karkashe mutane.
Sun yi rahoton kashe-kashen a jihohi 33 da Abuja, da suka hada da kisan jami’an tssro 221 da suka hada da sojoji 173, ‘yan sanda 39, NSCDC 3, duk a cikin wata uku.
Sannan kuma sun ce an kashe ‘yan ta’adda 845, ‘yan bindiga 502.
Mutum 941 aka kashe a Barno, 143 a Yobe, Taraba 113, Zamfara 444, Katsina 207, Sokoto 99, Kaduna 179.
Discussion about this post