Manajan Daraktan Riko na Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta (NDDC), Kemebradikumo Pondei, ya yi ikirari da bakin sa cewa hukumar ta yi wa naira bilyan 1.5 rabon-tuwon-gayya a tsakanin ma’aikatan ta, a matsayin tallafa musu lokacin zaman gida dole saboda Coronavirus.
Ya yi wannan furucin ne a lokacin zaman binciken yadda wata naira bilyan 40 ta yi fukafuki, kuma har yau aka rasa kan bishiyar da kudin suka dira.
Kwamitin Majalisar Dattawa da aka nada na mutum bakwai tun a ranar 5 Ga Mayu, shi ne aka dora wa nauyin binciken “yadda aka ragargaji kudade” a zargin da ake yi wa sabbin shugabannin rikon NDDC.
Majalisar Dattawa ta ce a cikin watanni uku, NDDC ta kashe naira bilyan 40 ba bisa ka’ida ba. Wannan kuwa kara haifar da zargi kan Hukumar daga bangaren masu hakki a karkashin ta.
“An kuma zargi Shugabannin Rikon NDDC da laifin yi wa ma’aikatan hukumar kwasar-karan-karan mahaukaciya, su na watsar wa a waje, ba bisa ka’idar korar ma’aikata daga aiki ba.”
Yadda Ta Kaya Da Shugabannin NDDC A Majalisar Dattawa:
Shugaban Riko Pondie da mukarraban sa sun amsa gayyatar Kwamitin Bincike na Majalisar Dattawa a ranar Alhamis.
Daga cikin zarge-zargen da Shugaban Kwamitin Bincike Sanata Olubunmi Adetunmbi ya karanto a bainar jama’a, ya ce:
“An gano shugabannin NDDC sun yi kaca-kaca da naira bilyan 3.1 tsakanin Oktoba 2019, zuwa Mayu 2020, kudaden da suka rubuta cewa an kashe wajen tallafin Korona ga ma’aikatan hukumar.”
Rabon-tuwon-gayyar Naira Bilyan 3.1:
Rahoton ya bayyana ta bakin fallasar da Sanata Adetumbi cewa, “mutum daya ya jidi naira milyan 10, mutum biyu sun wafci naira milyan 7 sun raba, wasu mutum 148 sun daka wasoson kudi, suka raba wa kowa naira milyan 3 a tsakanin su. An kacalcala wa mutum 157 kowanen su naira milyan 1.5, sai kuma wasu mutum 497 da aka yi wa likin naira milyan 1 kowanen su. Wasu mutum 464 sun yi gafiya tsira da na bakin ki da naira 600,000 kowanen su.”
Su ma ‘yan sanda ba a bar su a baya ba, ba su zama ‘yan kallo ba. Rahoton ya ce an ba su naira milyan 475 domin su sayi takunkumin rufe fuska.
Da ya ke maida bayani a kan wadannan kudade, Shugaban Riko na NDDC, Pondie ya ce naira bilyan 1.5 ce kadai aka raba wa ma’aikatan, duk kuwa da cewa ana biyan kowanen su albashi.
Ya ce sauran kudaden na wadanda ake raba wa matasan Neja Delta ne.
“An bai wa matasan Neja Delta kudaden domin rage musu radadin kuncin zaman gida dole a lokacin Korona. Kun san matasan duk zauna-gari-banza ne. Ana ba su kudaden don kada su rika tayar da fitintinu.” Inji Pondie.
‘An raba wa matasan kowace shiyyar sanata naira milyan 5, su ma matan shiyyar milyan 5, haka su ma nakasassun kowace shiyya an raba musu naira milyan 5.” Inji shi.
Ya kara da cewa, “sauran kudaden kuma aka kashe wa ma’aikatan hukumar.”
“Mun yi amfani da kudaden domin hidimar kan mu. Mu fa ma’aikatan NDDC ne, mu na bukatar kudade domin jin dadin rayuwar mu.” Inji shi.
Da aka tambaye shi dalilin bai wa ‘yan sanda naira milyan 475, sai Pondie ya ce, shugabannin ‘yan sanda daga can kololuwa suka rubuto sakon neman tallafi, “mu kuma muka tallafa musu.”
Mataimakin Daraktan Riko, Cairo Ojougboh, ya yi karin bayanin cewa kudaden da aka bai wa ‘yan sandan, na wadanda ke jihohin Neja-Delta guda tara ne, ba na ‘yan sandan kasar gaba daya aka raba wa kudin ba.
Za a ci gaba da saurare a ranar Juma’a.
Discussion about this post