Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ya bayyan kamuwa da kwayoyin cutar Korona ranar lahadi.
Ministan ya ce ” Bayan gwajin cutar da aka yi min wanda na hudu kenan, an samu na kamu da kwayoyin cutar Korona. A dalilin haka tuni har na garzaya wurin killace masu dauke da cutar domin samun kula.
” Haka rayuwa yake, wasu su tsallake , wasu kuma a samu akasi. Ina barar addu’ar Allah ya bani lafiya daga gareku.
Minista Onyeama ya shiga jerin manyan kasar nan da suka yi fama da cutar Korona da suka hada da, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, Gwamnan Oyo, Seyi makinde, Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu da Gwamna Okezie Ikpeazu.
Sannan kuma shuagaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa Abba Kyari da ya rasu da kuma tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 653 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –115, Kwara-85, Enugu-80, FCT-78, Rivers-36, Ondo-35, Oyo-30, Katsina-28, Kaduna-19,Abia-19, Nasarawa-18, Filato-17, Imo-16, Ogun-9, Ebonyi-9, Benue-9, Kano-9, Delta-8 Bauchi-7, Ekiti-6, Gombe-4, Bayelsa-4, Adamawa-4, Osun-4, Cross River-1, Yobe-1, Borno-1 da Zamfara-1.
Yanzu mutum 36107 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 14938 sun warke, 778 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 20,391 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 13,341 FCT – 2,957, Oyo – 2,106, Edo – 1,885, Delta – 1,423, Rivers – 1,516, Kano – 1,395, Ogun – 1,168, Kaduna – 1,118, Katsina –1,087, Ondo – 912 , Borno –598, Gombe – 544, Bauchi – 529, Ebonyi – 655, Filato – 620, Enugu – 675, Abia – 479, Imo – 452, Jigawa – 322, Kwara – 535, Bayelsa – 322, Nasarawa – 254, Osun – 332, Sokoto – 153, Niger – 145, Akwa Ibom – 162, Benue – 194, Adamawa – 115, Anambra – 101, Kebbi – 88, Zamfara – 77, Yobe – 64, Ekiti – 84, Taraba- 30, Kogi – 5, da Cross Rivers – 13.