Minista Akpabio ya maida martani game da zargin yunkurin cin zarafin tsohuwar shugabar Hukumar NDDC

0

Ministan Harkokin Neja-Delta, Godswill Akoabio, ya waske wa tambayar jin ta ba kin sa, dangane da yunkurin yin lalata da tsohuwar shugabar Hukumar NDDC, Nunieh ta yi masa.

Nunieh a wata hira da Gidan Talbijin na Arise TV, ta yi ikirarin cewa Akpabio ya gayyace ta gidan shakatawar sa, inda ya yi yunkurin murkushe ta, amma ta gaura masa mari.

“Dadin-baki ya rika yi min wai zai tabbatar cewa an maida ni kan mukami na. Daga nan ya kai hannu zai kankame ni. Ni kuma na gaura wa jarababbe mari.” Inji Nunieh.

Har tinkaho ta rika yi a lokacin tattaunawar, ta na cewa ita ‘yar Neja-Delta din da ta taba falla wa Akoabio mari.

Sai dai kuma a ranar Talata a hirar sa da PREMIUM TIMES, Ministan ya kauce wa yin fito-na-fito da matar.

“Kada mu maida kai ga labaran nishadin-hululu da kutunguilar neman ganin bayan wani. Gara mu maida hankali kan abin da zai kawo ci gaba ga Yankin Neja-Delta, domin shi ne abin da na sa gaba.

“A matsayi na na Ministan Najeriya, na wuce zubar da girma na ina yamadidi da batun wani mutum. Aikin bunkasa Yankin Neja-Delta ne a gaba na sai kuma taimakawa wajen ganin ci gaban kasar nan a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin hirar, Akpabio ya rika yin dogon bayani kan halin tabarbarewar da ya gada a Hukumar NDDC, da kuma kokarin da ya ke yi wajen bunkasa yankin ta hanyar gudanar da ayyukan more rayuwa, bunkasa noma, inganta ilmi da samar da aikin yi a yankin na Neja-Delta.

Sannan kuma ya yi karin haske akan dauke binciken da ake yi a hukumar NDDC, wanda ya ce yanzu haka wasu da suka nemi danne kudade har sun kammala titina kusan 70, saboda kawai sun ji an fara bincike.

Akpabio ya tabo batun rikicin da ya dabaibaye NDDC ya na Mai cewa, “bai yiwuwa a ce kamar ni ina shugabancin Ma’aikatar Bunkasa Neja-Delta, kuma a ce ba a samu ci gaba ba.

A ranar Litinin, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Nunieh ta fara zargin Minista Akpabio da shirya gidogar bilyoyin kudade. Sai kuma kokarin da ya yi na yi mata girkar yin rantsuwar sirri cewa ba za ta fallasa duk wata harkalla da ya yi ba.

Bayan nan ne kuma ta fallasa cewa har danne ta ya nemi yi, amma ta kwantsama masa mari.

Tsohuwar Shugabar Riko ta Hukumar Raya Jihohin Neja Delta (NNDC), Joy Nunieh, ta zargi Ministan Ma’aikatar Kula da Neja-Delta, Godswill Akpabio da harkallar satar makudan kudade.

Nunieh ta ce a cikin ‘yan watannin da ta yi ta na rikon-kwaryar hukumar, Minista Akpabio a matsayin sa na Ministan Neja-Delta, ya yi ta kokarin tirsasa ta yin rantsuwa a asirce cewa ba za ta fallasa duk wata cuwa-cuwa, harkalla, wuru-wuru, kamaya-maya, lodi da jidar kudaden da aka yi ko za a yi ba.

“Misali, akwai lokacin da ya ce min na shirya takardar bayar da kwangilar bogi ta raba kayan agaji ga al’ummar Neja-Delta da albaliyar ruwa ya yi wa barna.” Inji Nunieh.

Ma’aikatar Neja-Delta da Akpabio ke shugabanci dai ita ce ke kula da ayyukan Hukumar NNDC.

Tsohuwar shugabar ta NNDC, ta shaida wa manema labarai bayan ta fito daga bayyanar da ta yi a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Binciken NNDC cewa, da ta kuskura ta bi son ran Minista Akpabio ta yi duk abin da ya ke so ta rika yi, to da yanzu ta na can daure a kurkuku.

Ta ce Akpabio ya yi duk wani kokari domin ya tirsasa ta yin rantsuwar ba za ta tona masa asiri ba, amma ta ki.

Tuni wannan bidiyo da Gidan Talbijin na Channels ya nuna, ana ta watsa shi a soshiyal midiya.

Ta ce sau uku Akpabio ya na tirsasa ta domin ta yi rantsuwar ba za ta tona masa asiri ba.

Ta kara da cewa da ta ki yin rantsuwar-,kaffarar,-Akpabio, sai aka rangada fadar shugaban kasa aka gurfana a gaban Sarki Abba, Hadimin Shugaban Kasa a Harkokin Cikin Gida.” Shi ne ya sasanta mu.

Nunieh ta ce tsoro ta ji za ta iya zaman kurkukun shekara biyar cur idan Akpabio ya gina mata rijiya ta rufta.

Ta ce za a iya kama ta a karkashin Dokar Ka’idojin Bayar Da Kwangiloli. Alhali ba ta iya kare kan ta, shi kuma Akpabio ya tsallake rijiya abin sa.

“To sai bayan da na ki amincewa na yi wa Akpabio rantsuwar-kaffara ce sannan ya fara kulla fuggun ganin an cire ni daga kan mukamin.

“Ya ce sai ya xire ni. Daga nan kuma ya fara watsa farfagandar bata min suna da zubar min da kima.” Inji ta.

Kokarin da Premium Times ta yi domin jin ta bakin Kakakin Akpabio, Anietie Ekoong ya ci tura, domin har yau ba a maido amsar tes din da aka tura masa ba.

Takun-saka Tsakanin Akpabio Da Nunieh:

Nunieh ta zama Shugabar Rikon NNDC bayan an cire Akwagaga Enyia cikin Octoba 2019.
Sai dai kuma ita ma din an cire ta watanni hudu bayan nada ta, bayan rika samun bayanan salwantar makudan kudade.

Daga nan ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Kemebradikumo Pondei, a madadin ta.

Pondei ne a waccan Alhamis da ta gabata, ya shaida wa Kwamitin Bincike a Majalisar Dattawa cewa, sun kassafa naira bilyan 1.5 a tsakanin su, a matsayin tallafa wa kan su da agajin zaman gida lokacin Coronavirus.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Minista Akpabio ya kitsa algungumancin cire Nunieh daga shugabancin NNDC, aka nada Kemebradikumo.

Mutanen da ke da masaniyar takun-saka tsakanin Akpabio da Nuneih, sun ce mutanen biyu ba su jituwa a tsakanin su.

Yayin da ake tattaunawa da ita, ta ce Akpabio bai taba sa wa takardun ta hannu ba. Sai dai kawai ya hada baki da wasu ‘yan barandan sa su rika shirga karkallar fitar da makudan kudade.

“Ina sane na ki bin sa zuwa Taron Majalisar Zartaswa, domin na rigaya na san irin mummunar gidogar harkallar da ya shirya wa Shugaban Kasa. Na san Dokar Kwangila za ta iya kama ni da laifi, har a daure ni shekaru biyar.”

Nunieh ta ci gaba da bayyana dalla-dallar kwangilolin gidoga da Akoabio ya rika shiryawa. Kuma ta ce duk wasu kudade da za a fitar, sai da sanin sa.

Share.

game da Author