Wata Mata mahaifiyar ‘ya’ya uku mai suna Oluwayemisi Ajakaye ta shigar da kara a kotun majistare dake Mapo a Ibadan, tana rokon kotu ta raba auren su da ya shekara 12.
Oluwayemisi ta kawo kukanta kotu ne saboda yadda mijinta ke cin zarafin ta kullun ranar Allah.
Ta ce mijin ta Segun na kiran ta alade sannan har kwatanta da wasu munanan dabbobi yake yi.
“Segun har Akuya Yana Kira na sannan ya lakadamun dukan tsiya.
” Sannan sam bani da natsuwa da kwanciyar hankali a gida na domin a kulum ni fasikace dake kwana da Maza a waje. Sannan ko mahaifiyata bata tsira ba domin a duk lokacin da ya yi mata waya sai ya yi barazanar kashe ta.
Oluwayemisi ta nuna wa kotun tabo da raunin dukar da ta ke sha a wajen mijinta Segun
Ta roki kotu da ta raba aurenta da Segun cewa ta gaji da zaman ukuba haka nan.
Segun bai zo kotu ba duk da cewa an kai masa sammace har sau uku.
Alkalin kotun Ademola Odunade ya raba auren sannan ya bai wa Oluwayemisita rikon ‘ya’yan su uku da suka haifa tare.
Alkalin ya umurci Segun ya rika biyan naira 15,000 duk wata domin ciyar da ‘ya’yan.