MATSALAR TSARO: Majalisar Dattawa ta nemi Buhari ya tsige Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya

0

A karo na biyu cikin 2020, Majalisar Dattawa ta sake yin kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige Shugabannin Tsaron Najeriya, ko kuma su sauka domin a nada sabbi kuma masu sabbin dabarun samar da dawwamammen tsaro a kasar nan.

Hakan ya biyo bayan tsinkayen da suka sake yi dangane da yawan asarar rayukan fararen hula da na sojoji da ake ci gaba da yi, har da ma sauran jami’an tsaro a kasar nan.

Sanata Ali Ndume daga Jihar Barno, kuma Shugaban Kwamitin Tsaro, shi ne ya bayar da shawarar saukar manyan shugabannin tsaron, kuma Majalisa ta amince.

Wannan kira ya zo kwana biyu kacal bayan da ‘yan bindiga suka kashe sojoji 17 a Karamar Hukumar Batsari, cikin Jihar Katsina, kuma suka raunata wasu sojoji 28.

Cikin wadanda aka kashen har da Manjo, Kaftin da Laftanar.

Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES ta buga rahoton yadda wasu sojoji 356 suka mika takardun yin ritaya bisa dalilin da suka ce, “aikin ya fita daga ran su.

Ndume ya nuna damuwa dangane da yadda ake yawan kashe sojoji. Hakan inji shi zai kara haifar da barazanar tsaro a kasar nan.

Shi da sauran wadanda suka yi jawabi sun gode wa shugabannin tsaron yanzu bisa ga kokarin su na tsawon shekaru. Amma dai sun yi kira su sauka haka nan tunda an ga iyakar gudun ruwan su.

Share.

game da Author