MATSALAR TSARO: Buhari ya aika Shugabannin Tsaron Kasa a Yankin Arewa maso Yamma

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya tura jiga-jigan shugabannin tsaron kasa a jihohin Arewa maso Yamma, inda ‘yan bindiga suka hana zaman lafiya, domin ganawa da masu fada-a-jin yankin, saboda tattauna mafitar kalubalen matsalar tsaron da ake fuskanta.

Sufero Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Adamu ne ya bayyana haka, ya ce taron ganawa da masu ruwa da tsakin zai sake nazarin tsare-tsaren tsaro da kuma bijiro da sabbin dabarun kawo karshen hare-hare da tayar da zaune tsayen da ya mamaye Arewa maso Yamma.

Adamu ya yi wannan jawabi a lokacin da shugabannin tsaron suka kai ziyarar ban-girma a Fadar Mai Martaba Ssrkin Gusau, Ibrahim Bello a ranar Alhamis.

Adamu ya kara da cewa kokarin da gwamnatin tarayya ke yi domin ta magance matsalar tsaro, ba a jihar Zamfara kadai ya tsaya ba, har ma da sauran jihohin Arewa maso Yamma baki daya.

“Mun zo Zamfara ne a yau, saboda Shugaba Muhammadu Buhari ya ba mu umarni tare da gargadin cewa mu tabbatar mun kawo karshen wannan rikici a yankin nan.

“Ya ce mu zo mu zauna tare da ku domin mu gano sauran wuraren da ake fuskantar kalubalen da har yanzu ya ki ci ya ki cinyewa, domin a shawo kan lamarin.”

Ya ce idan ana wannan taron, za mu tattauna duk wani abu da ke kawo tarnaki wajen samar da tsaro a Arewa maso Yamma domin neman mafita.

A nasa jawabin, Sarkin Gusau ya gode wa manyan jami’an tsaron, kuma ya yi addu’a Allah ya bada nasarar wannan sabon hobbasa da aka yi.

Sai dai ya yi korafin yawaitar ‘yan leken asiri da ke cikin jama’a, masu hada baki da ‘yan bindiga.

“Saboda mu na da labarin cewa akwai mutanen da ke daukar gidaje su na damkawa haya ga ‘yan bindiga.

Daga nan sai ya nemi a kafa dokar da za ta rika hukunta irin wadannan mutanen.

Cikin tawagar Sufeto Janar, har da Shugaban SSS, Yusuf Magaji, Ahmed Rufai ns NIA da AVM Muhammad na DI da sauran wasu jiga-,jigan tsaro.

Share.

game da Author