Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bada gudunmawar naira milliyan 100 fon gina jami’ar musulunci a Zamfara.
Matawalle ya mika wannan kudi ne a lokacin da shugabannin kungiyar Jama’atul Izalatil Bida Wa Ikamatussunnah, JBWIS karkashin shugabancin Sheikh Bala Lau suka ziyarce shi a garin Gusau.
Ya Yi Kira ga gwamnonin da attajirai musamman na yankin Arewa su bada gudunmawar su domin samun nasarar gina wannan jami’a.
Matawalle ya koka kan matsalolin rashin ilimi da rashi tarbiyyarta da ya yi wa yara yanzu katutu musamman a yankin Arewa.
“Mun koma wadanda basu kwaunar juna da kishin yankin mu. Ba mu son juna. Yanzu ya kai ga a yankin mu na Arewa nan ne ayyukan ta’addanci ya fi tsanani saboda yadda kauna da son juna ya fita fut daga zukatan mu.
” Ku duba yadda matsalar ‘ yan bindiga ya fi karfin mu a Arewa, Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a tsakanin mu, sace-sace, Kashe- kashe da ba a sn mu da shi ba duk yanzu sune muke fama da su saboda kiyayar da ta shiga tsakanin mu.
“Na Yi kokari wajen dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara kuma zan ci gaba domin maida hankali akan haka domin mutanen mu koma cikin walwala kamar da.
” Yanzu rokona garrku shine ku ci gaba da fadakar da iyaye wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yan su sannan kuma ku malamai a maida hankali waken ilmantar da yara yadda ya kamata.
A jawabin sa jagoran tawagar, kuma shugaban kungiyar JIBWIS, Sheikh Bala Lau ya ce kungiyar ta kawo wa gwamnan jihar ziyara ne bayan duba wani makaranta da tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya ba kungiyar JIBWIS a garin Shinkafi.