Mata a dage a yi kiba, maza sun fi raja’a ga mata masu kiba – Zauren Mal Mudi

0

Masu karatu da dama da suka yi sharhi kan tambayar da malam Mudi yayi cewa masu karatu su fadi rayoyin su game da (Mace mai kiba (Bakutu) ta fi daraja miji ko saurayi fiye da mace Siririya ‘Yar filinge).

Kashi Casa’in bisa Dari na wadanda suka ta fadi ra’ayoyin su sun bayyana cewa lallai mata masu kiba sun fi dadin sha’ani. Baya ga ladabi da biyayya ga miji akwai su da hakuri, kuma suna da kwazo wajen raya sunnah.

Da yawa sun bayyana cewa, mata sirara, ba su da kunya, tigalallu ne da kadifirin tsiya,sannan ga jijji da kai sannan basu da natsuwa kamar yadda mace mai kiba ta ke da shi.

Sai dai kuma da dama sun bayyana cewa akan samu wasu mata masu kiba da dasu da tsafta. Mata marasa kiba sun fi tsafta.

1 – Bala Magaji Gusau

2 – Sadiq Sagir Sharada

3 – Abubakar Mustapha Kiru

4 – Abubakar Gumbari

5 – Mohammed Bashar Tookoor

Ga dai abinda wasu daga cikin masu karatu suka fadi:

Bala Magaji Gusau

Mace marar kiba tafi mai kiba. Wajen lafiyar jiki.domin mafi yawa zaka same su matsalolin hawan jini .ciwon suga. Rashin haihuwa .(2)ga kuma saurin tsufa. It’a ko siririyar mace bata saurin tsufa gata da juriya.ko zakuga mafiyawan matan shuwagabanni a nigeri ai basuda kiba. (3)aiko wajen dunka suturar sawa .Kayan macce mai kiba. Sunfi wuyar dunkawa.

Sagir Sadiq Sharada

Mata masu kiba ko mace Mai kiba tana tasirantuwa a zuciyar Mai gidanta da yawa da yawa fiye da mace siririya (figatsiyau) abisa hujjojina kamar haka idan muka dubi ta bangaren tsafta da kwalliya zaka tarar mace Mai kiba ako da yaushe tana kokarin yin wanka akai saboda yanayin jikinta baya bukatar zafi wannan ya taimaka mata wajen yin tsafta da barin jiki Babu wari a maimakon haka zaka tarar da hada da kwalliya zaka tarar da ita kullum tsaf tsaf take, sannan idan ka dubi yanayin rashin lafiya da aikace aikacen gida abin zai matukar bayar da mamaki cewa mace Mai kiba tafi siririya yawan wanke wanken abubuwan da gida yake bukata Kama daga gidan shi kansa zuwa bandaki dakin girki da kayan sawa da sauran abubuwan da ake wankewa yanayin jikin matar aure Yar lukuta baya hana ta dukkan aikace aikacen gida cikin sauri fiye siririya dukkan Wanda yake da mace Yar lukuta yasan da haka, ita kuma siririya (figatsiyau) da akwai ganda da son jiki kamar mage.

Sannan a bangaren rashin lafiya bata fiye Laulayi ba d da saurin rashin lafiya kamar siririya ba,
Sannan a zamantewarka bata da Saurin fushi kamar siririya wacce magana kadan sai masifa da hargowa sannan idan kayi baki Mai kiba tafi Haba Haba da sakin fuska ga bakinka, sannan ko a yan’uwanka zakaji sunfi yabonta saboda da akwai da haba haba da jama’a, ba kamar yar siririya ba wajen rashin ko in kula da yan’uwanka sannan zaka tarar tafi alkinta maka dukkan Abinda idan aka wani ya gani zai dauka domin bataye son sa’insa ba, sannan muryar mace Mai kiba tafi ta siririya Zaki da kwantar da Rai sau da tari idan kaji muryar mace Mai Zaki zaka tarar da Mai kiba ce sannan tana kunya da Kara akanka da Kuma wayanda suke tare da ita saboda batason fishi da yawa da yawa yawan wayanda suka fara auren mace siririya daga baya suka auri Mai kiba zaka tarar Mai kibar tafi shiga ran Mai gidan akan siririya saboda komai nata Mai sauki wajen jinsa sannan daga karshe a bayanan masana halayyar Dan Adam sun gabatar da wani binkice inda suka gano cewa mace Mai kiba tafi mace siririya iya girki, kwalliya tsafta da iya rikon miji sannan suka tabbatar da cewa mace Mai kiba magidanta sunfi Jin dadin aure dasu da Kuma nuna kulawa ta musamman fiye da mace siririya an wallafa haka a gidan radio freedom dake kano, a tabakin nasiru salisu zango.

Abubakar Mustapha Kiru

Mace mai ƙiba yawanci sunfi daraja miji, wannan a tunanina yasamo asali ne da watakila:

1. Maza basa yayin ɓakutu.

2. Suna wahalar auruwa…

3. Basu cika lafiya ba bayan saboda tarin kitse

4. Jikinsu nada nauyi sosai…

5. Jikinsu baya dadewa suke rugujewa kamar tarin yashi yayin da ake ruwan sama…

Sanin haka dama wasu abubuwan daban lissafo ba, yakan sanya su kasance masu hakuri, domin sunsan cewa

1. Ba’a yayinsu

2. Idan sukayi wargi har aka sakesu zasuyi wuyar sake auruwa…

3. Saboda nauyin jikinsu, su takansu ma sukeyi balle su jawo rigima da mai gida…

4. Suna taka tsantsan da lafiyarsu domin sun san cewa taɓasu kaɗan kan jawo musu rikicewar lafiya.

ITA KUWA YAR FILINGI!!!

Hmmm abin ba’a cewa komai, domin kuwa;
1. Tasan cewa maza na yayin ta, saboda haka ba ruwanta , jan fada ne da ita kamar yar dambe duk da bata da karfi.

2. Kuma saboda haka tasan sarai zata ƙara samun manemi, sai kaga har damara takeyi da dambe da mai gida da makwaɓta.

3. Yar filingi Allah ya yassare mata lafiya, saboda jikinta babu kitse saboda haka neman fada ne da ita.

4. Bata da nauyi kamar takarda take, duk da bata da karfi ta fiye neman fada domin ji take rashin nauyi karfi ne, sai an hada jiki ido ke raina fata.

5. Yar filingi kan dade tayi ƙarko sabanin yar uwarta wato ɓakutu koda kuwa ta haihu ne.

Wadannan dalilai, zasu nuna maka/ki cewa, yar filingi tafi yar lukutaye neman fada, domin shi faɗa da rigima da jiji da kai dalili ne kesanyawa, waɗannan dalilai kuwa suno na zayyano a sama.

Muhammad Zailani

Eh zan iya yarda da cewa mai qiba tafi girmama miji fiyeda siririya saboda dalilai kamar haka:

Na farko mai qiba tana ganin cewa qila maza basu cika yayinsu ba don haka wanda ta samu zata dinga riritashi tana bashi kulawa ta yadda bazata yarda wata ‘yar filingen ta qwace mata shi ba.

Sannan na biyu saboda dayawa suna ganin cewa maza sunfi son siririya don ita mai qiban tafi saurin tsufa da saurin ragwabewa, dona haka yasa take iya bakin kokarinta don ganin ta farantawa mijin ba tare da ya kai hankalimshi ga wata a waje ba musamman mara qiba.

Sannan dalilin da yasa mara qiba take wulakanci shine don tana ganin ita jikinta mai jurewa ne ba kuma ya saurin nuna tsufa, hakan yasa take sakwa sakwa wurin kulawa dashi don tana tunanin koda ta barshi bazatayi wahakar samun wani ba.
Sannan tana yi ne don taga cewa yawancin maza suna ikirarin cewa maza sunfi yayinsu don basa saurin rakwabewa

Sagir Sadiq Sharada

Mata masu kiba ko mace Mai kiba tana tasirantuwa a zuciyar Mai gidanta da yawa da yawa fiye da mace siririya (figatsiyau) abisa hujjojina kamar haka idan muka dubi ta bangaren tsafta da kwalliya zaka tarar mace Mai kiba ako da yaushe tana kokarin yin wanka akai saboda yanayin jikinta baya bukatar zafi wannan ya taimaka mata wajen yin tsafta da barin jiki Babu wari a maimakon haka zaka tarar da hada da kwalliya zaka tarar da ita kullum tsaf tsaf take, sannan idan ka dubi yanayin rashin lafiya da aikace aikacen gida abin zai matukar bayar da mamaki cewa mace Mai kiba tafi siririya yawan wanke wanken abubuwan da gida yake bukata Kama daga gidan shi kansa zuwa bandaki dakin girki da kayan sawa da sauran abubuwan da ake wankewa yanayin jikin matar aure Yar lukuta baya hana ta dukkan aikace aikacen gida cikin sauri fiye siririya dukkan Wanda yake da mace Yar lukuta yasan da haka, ita kuma siririya (figatsiyau) da akwai ganda da son jiki kamar mage.

Sannan a bangaren rashin lafiya bata fiye Laulayi ba d da saurin rashin lafiya kamar siririya ba.

Sannan a zamantewarka bata da Saurin fushi kamar siririya wacce magana kadan sai masifa da hargowa sannan idan kayi baki Mai kiba tafi Haba Haba da sakin fuska ga bakinka, sannan ko a yan’uwanka zakaji sunfi yabonta saboda da akwai da haba haba da jama’a, ba kamar yar siririya ba wajen rashin ko in kula da yan’uwanka sannan zaka tarar tafi alkinta maka dukkan Abinda idan aka wani ya gani zai dauka domin bataye son sa’insa ba, sannan muryar mace Mai kiba tafi ta siririya Zaki da kwantar da Rai sau da tari idan kaji muryar mace Mai Zaki zaka tarar da Mai kiba ce sannan tana kunya da Kara akanka da Kuma wayanda suke tare da ita saboda batason fishi da yawa da yawa yawan wayanda suka fara auren mace siririya daga baya suka auri Mai kiba zaka tarar Mai kibar tafi shiga ran Mai gidan akan siririya saboda komai nata Mai sauki wajen jinsa sannan daga karshe a bayanan masana halayyar Dan Adam sun gabatar da wani binkice inda suka gano cewa mace Mai kiba tafi mace siririya iya girki, kwalliya tsafta da iya rikon miji sannan suka tabbatar da cewa mace Mai kiba magidanta sunfi Jin dadin aure dasu da Kuma nuna kulawa ta musamman fiye da mace siririya an wallafa haka a gidan radio freedom dake kano, a tabakin nasiru salisu zango.

Wasu daga cikin ra’ayoyin masu Karatu

Sir Awwal Danmasanin Facebook

Ai da Maza da mata marasa kiba akasari sunfi fitina, dalili kuwa shine suna ganin idan basu yi haka ba za’a Raina su saboda ana musu kallon marasa kuzari. Musamman Mata sirarai Suna yauwaita fitina ne a matsayin kariyar Kai wato “defensive mechanism” a turance.

Kuma bincike da yawa cikin karatun kula da halayyar Dan adam suna tabbatar da haka.

Amir Ahmad Gano

Mace mai kiba tafi daraja miji saboda ta gamsu cewa idan mijin ya kubuce mata ba lalle ne ta Sami wani kamar sa ba, ita kuwa siririya gani takeyi ko yaushe ta rabu da mijinta zata iya samun Wanda ya fishi baya da haka, ita katuwa bata fiyyya sarrrafuwa ba wajen wassani na aure to sai ka ga tana Jan mutuncin ta gun mijinta ita kuwa siririya tana sarrafuwa Kai har daukar yaro miji na iya yi mata to sai da maida kanta kamar yaron da aka shagwaba

Abubakar Gumbari

Maganganu dayawa sun gabata amma gareni idan zanyi ba’asi akan mace yar lukuta fashimtata dasu tana da yawa

Bakutu ko yar lukuta wani nau’ine Na mace wadda namiji yafi samin gamsuwa dasu, alal hakika mafiya yawan maza sunyi rinjaye akan San mace yar lukuta bisaga dalilansu kamar haka.

Na daya mace yar lukuta tanada siffa mai daukar hankali gata da godiyar Allah, duk karancin samunka bazata nunakaba

Sannan Allah yamusu hakuri dukda sunada siffa ta kwata da karfi amma sunfi yan fingilgil hakuri.

Bakuta akwaisu tausayi ga zaman lafiya amma hajiya fingil akwai balbalin bala’i gata kamar ka hureta ta fadi

Fingil akwai zakin baki babu karfi ga wayo da sanna mallake miji ko saurayi

Da wannan bayanin zan takaita babu gami tsakanin yar lukuta da fingili

Ismail Abdallah

Tabas anfi samun ,mata masu kyau .A wajan siririya ,amma mace siriri akwaita da matsalar kamar haka ,(1) wajan haihuwa (2) fada(3) kunlin taganin idan mijinta yasa keta to tanada kyawun jikinda wani zaice yana sonta, shiyasa da yawansu basu girmama mazansu.Haka ma mata masu kiba.Suma sunada nasu abubuwa kamar ka .Nafarko (1) hakuri (2) biyayya (3) kulada miji musamman wajan kwanciyar aure (4) galibi ba a cika samun mace me kiba, tana shan wuya wajan haihuwa ba(5) Galibi ta biyayyane ga mijinta sabuda tasani tanada kiba ,bakowa zai auretaba farat daya ba.

Mohammed Bashar Tookoor

A gaskia mata marar kiba sunfi shiga ran mutum dan ko wanka ma kaga marar kiba tayi yapi hawanta amma ita maikiba zakaganta kamar buhu ko ina ciki tupapin ma wani shape haka amma yar silinde ko zakaga tupqn sun mata coca cola shape, sa annan mapi yawancin masu kiba basu cika yawan samariba akasarima idan kaga mata marar kiba ko ga unguwa zakaga zunfi jan hankalin samari kuma sunfi yawan samari #danawagani

Mun gode da ra’ayoyin ku.

Share.

game da Author