Majalisar jihar Kaduna, Karkashin Honarabul, Yusuf Zailani ta amince da da sabon kasafin jihar fa bangaren zartaswa ta aika da shi.
Majalisar ta amince da rage kasafin daga naira biliyan 259.25 zuwa naira biliyan 223.6.
Shugaban kwamitin Kudin majalisar Honarabul Ahmed Mohammed ya shaida cewa wannan jirkita kasafin kudi da gwamnati ta yi ya zama dole ganin yadda kasar ta fada cikin tabarbarewar arziki sanadiyyar annobar Korona da ake fama da a duk duniya.
Hnarabul Ahmed ya ce majalisar ta amince da rage kasafin da aka ware na manyan ayyuka daga naira biliyan N184, 105, 599, 693.28 zuwa naira biliyan 146, 112, 237, 760. 69. Haka kuma an rage kudaden da za a kashe na ayyukan yau da kullum daga
N77, 489, 480, 486.22 zuwa N77, 145, 220, 040.38.
Bayan amincewa da wannan sabon kasafi, sai kakain majalisar ya dage zaman majalisar zuwa 7 ga watan Yuli.
Majalisar bata kara ba kuma ba ta rage ko sisi daga alkaluman da fadar gwamnatin Nasir El-Rufai ta aiko mata da shi. Yadda kasafin ya zo haka ya koma. Kacokan din ‘yan majalisan sun yi na’am da tsarin fannin zartaswar kuma sun mika wuya.
Jihar Kaduna dai na samun gagarimin canji musamman a ayyukan raya jihar da manyan gine-gine da an yi dadewar gaske ba a taba samun irin haka ba.
Duk da rage kasafin da gwamnati ta yi, gwamnan jihar El-Rufai ya saha alwashin ya canja fasalin jihar Kaduna zuwa jihar da za a rika alfahari da ita a fadin kasar nan.
Discussion about this post