Mahara sun sace Diyar Dan majalisan dake wakiltar Dambatta a majalisar Kano

0

Mahara dauke da bindigogi sun dira har gidan dan majalisar dokoki dake wakiltar Dambatta a majalisar Kano, sun yi awon gaba da diyar sa.

An sace Diyar Honarabul Murtala Musa, Juwairiyya, a gidan sa dake kauyen Kore, karamar Hukumar Dambatta

Juwairiyya mai shekaru 17 na karatu a makarantar gwamnatin dake Jogana, jihar Kano.

Honarabul Murtala ya shaida cewa shi ne maharan ke fako, da suka zo gidan ba su iske shi ba sai suka daddaure yayansa da suka yi zaton shi ne.

” Daga baya sai suka waske da Diya ta. Amma kuma har yanzu basu kira ba ballantana su fadi abinda za a basu.

Share.

game da Author