Dakataccen Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, ya karya wani sabon zargin cewa wai ya karkatar da wasu makudan kudi da ya kwato har naira bilyan 329 da aka sata a NNPC.
Lauyan sa Wahab Shittu ya ce Magu bayan ya kwato kudaden daga hannun manyan dillalan fetur, ya maida su a asusun NNPC din.
Wahab Shittu ya ce bayan Magu ya maida kudaden, har rasidin shaidar karbar kudaden NNPC ta bai wa NNPC.
“Maganar gaskiya surutan wai Magu ya danne naira bilyan 329 na NNPC da ya karbo daga hannun manyan dillalan mai, zancen banza ne kawai.
“Magu ya kwato kudin kuma ya maida su asusun NNPC ta hanyar ‘remita’, har ma rasidi suka ba shi na shaidar karbar kudaden.”
“NNPC ce ta nemi EFCC ta kwato mata kudaden ta a hannun manyan dillalan mai. Ta karbo kuma an maida kudin a asusun NNPC din. Har rasidi na nan ajiye, a matsayin shaida.
“Don haka ta ya za a ce Magu ya danne kudaden da ko asusun wani ba su shiga ba, sai kai-tsaye asusun NNPC?
Daga nan ya ce Magu ba zai kara zura ido ana kala masa kage da kazafi da sharri ba. Duk zargin da aka yi masa zai rika maida raddi.
Duk wanda ya yi masa kan kara, zai yi masa na itace.
Dama cikin makon da ya gabata, Magu ya kalubalanci Malami da fito-na-fiton ya kawo shaida guda daya tal inda ya karbi toshiyar baki.
Dakataccen Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, ya kalubalanci Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kawo shaida ko da guda daya tal inda ya azurta kan sa da kadarar da ya kwato daga barayin gwamnati, ko kuma shaidar ya karbi toshiyar baki domin hana binciken wasu mabarnata.
Magu ya yi wa Malami wannan fito-na-fito ne, yayin da ya ke amsa tambayoyin zargin azurta kai daga Kwamitin Bincike, sanadiyyar zargin da Minista Malami ya yi masa.
Cikin makon da ya gabata Malami ya sanar cewa an dakatar da Magu ne bisa umarnin Shugaba Muhammdu Buhari.
Bayan damke Magu, ya shafe kwanaki 10 a tsare kafin a sake shi.
An rika kai shi Fadar Shugaban Kasa ya na amsa tambayoyi a gaban mambobin Kwamitin Ayo Salami.
An rika fallasa zarge-zargen yin sata-ta-saci-sata da Malami ya yi wa Magu.
Yayin da Magu ya ke karyata zarge-zargen da aka yi masa, shi ma ya karkato akalar sa, inda ya rika fallasa zargin rugumutsin harkallar da ya Malami ya rika tsbkawa.
PREMIUM TIMES HAUSA ts buga zargin da Magu ya yi cewa Malami ne ya gurgunta kokarin da EFCC ta yi domin dawo da tsohuwar Ministar Kudi, Deizani Allison-,Maduekwe domin ta fuskanci shari’a a Najeriya.
Sannan kuma Magu ya yi zargin cewa Malami ya bada odar yin gwanjon kayan sata ga wani kamfanin da ke gaban alkali ana tuhumar sa da satar danyen man Najeriya.
Magu har ila yau, ya yi zargin yadda wata kantamemiyar tankar jirgin ruwa dankare da danyen man fetur ta nutse a cikin aljihun Malami, aka yi ta lalube amma har yau ba a gano ta ba.
Fito-na-fiton Magu Ga Malami:
“Wadannan zarge-zargen karairayi da sharri da kazafi da ka ke min, abin tir ne domin muradin ka kawai ka bata min suna, ka zubar min da mutunci.
“Ina kalubakantar Malami da ke zargi na, ya kawo shaida ko da guda daya ce tal, inda na azurta kai na da kudade ko kadarorin da na kwato daga hannun barayin gwamnati. Ko kuma ya kawo ko da wuri daya wata shaida mai tabbatar da cewa na karbi toshiyar bakin hana a binciki wasu barayi ko mazambata.” Inji Magu.
Magu ya zargi Malami da cewa Kwamitin Binciken Kudaden Da EFCC ts Kwato, wanda Malami ya kafa a baya, bai yi masa adalci ba. Don ko sau daya baa bai wa shi Magu din damar kare kan sa ko sau daya ba.