Kwararan Hujjoji: Kwankwadar manja baya warkar da Korona – Binciken Dubawa

0

Shin ko wane darasi ne muka dauka game da siddabarun cewa ‘Wankar gishiri na Kau da Kwayar Cutar Ebola’?

A wannan lokaci da duk kasashen duniya ke fama da annobar Korona wani dake yin sharhi a shafin sada zumunta ta yanar gizo
‘Facebook’ ya wallafa cewa kwankwadar manja na warkar da kwayoyin cutar Korona. A bayanan sa ya shaida cewa za a rika shan akalla cokali biyu duk safe, cewa yin haka zai dakile yaduwar cutar, sannan masu dauke da cutar ma duk za su warke idan suka dage da sha.

Sai dai kuma, bincike da DUBAWA ta yi ya karyata wannan zance na sa.

Karyace: Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ba ta saka manja a cikin jerin sinadarorin da ke samar da kariya daga Korona ba. Babu kuma wani binciken da zai nuna cewa zai iya dakile wa ko kuma warkar da kwayoyin cutar Korona.

A yanzu, babu wani ingantaccen magani ko allurar rigakafin Korona a duniya; sai dai masana kimiyyar magunguna na cigaba da gudanar da bincike da yin gwajin sinadarai domin samar da rigakafin cutar.

Cikakken Bayanni

Duk da bullowar wasu maganganu na karya da aka rika yadawa wai suna warkar da cutar, wadanda ke yada labaran karerayi kuma sun cigaba da yada karerayin su duk da cewa an yi ta sanarwar cewa har yanzu ana cigaba da kokarin hada maganin rigakafin cutar ne ba a kammala ba.

Wannan marubuci da ya wallafa labarin shan manja don Korona ya bayyana cewa mutum ya sha cokali biyu duk rana domin samun lafiya da kauce wa kamuwa da cutar.

Har ila yau ya ce ya samu tabbacin cewa manja na maganin Korona ne a shafin Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, duk da cewa bai saka tambarin dake nuna alamar hukumar ba a sakonsa da ya wallafa.

Bincike da aka gudanar

Manja mai ne da ake amfani dashi a kusan kullum musamman wajen yin abinci, sannan kuma ya wadata a kasar nan. Akan tatso shi ta hanyar matse kwayoyin kwakwa da aka fi sani da kwakwar manja. Amma kuma babu wani bincike da ya nuna wannan mai na warkar da cutar Korona ko kuma dakile yaduwar ta a nan Najeriya da kuma Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya.

Haka kuma babu wani kwararan hujja da mawallafin ya bada da zai nuna cewa akwai gaskiya a bayanan sa daga ko wasu fitattun masana ko kuma cibiyoyi da aka shaide su a aikin samar da kiwon lafiya ko kuma hada magunguna.

Bisa ga dukkan bayanan da aka bi dalla-dalla wanda ya rubuta babu inda ya nuna cewa WHO na da alaka da maganar sa ko masaniya a kai.

Sanna kuma babu wani sakamakon bincike da aka yi da ya nuna cewa kwankwadar manja cokali biyu na warkar da cutar Korona, haka kuma ko a kalaman sa da ya wallafa, akwai rikitarwa kamar haka; shin ko shan manjan na warkar da korona ne ko kuma yana dakile yaduwar ta ne?Wadannan sune wasu daga cikin matsalolin da aka samu da wannan rubutu na sa.

Shawarar mu da abinda muka gano

Bisa ga bincike da nazari da muka yi, mun tabbatar da cewa shan manja cokali biyu baya warkar da cutar Korona a jikin wanda ya kamu. Wannan zance kanzon Kurege ne domin bashi da asali. DUBAWA na yin kira ga mutane da su nesanta kansu daga haka. A tuna da wahala da matsalolin da ak shiga a lokacin da mutane suka rika wanka da ruwan gishiri wai kariya ne daga cutar Ebola.

Share.

game da Author