Kwamitin kare ‘Yancin ‘Yan jarida ta duniya, CPJ, za ta karrama mawallafin Jaridar PREMIUM TIMES, da wasu uku

0

Mawallafin jaridar PREMIUM TIMES, Dapo Olorunyomi na daga cikin fitattu kuma jajirtattun ‘yan jarida da kungiyar kare ‘Yancin ‘Yan Jarida ta duniya za ta karrama a wannan shekara, 2020.

Wadannan fitattun ‘yan jarda su shahara wajen yin bugun kirji don tsage gaskiya yadda take ba tare da tsoron fadawa tarkon gwamnatocin kasashen su ko kuma a muzguna musu a wajrn aikin su.

‘Yan jaridan hudu da za a karrama sune,

Dapo Olorunyomi – Dapo Olorunyomi ne mawallafin jaridar PREMIUM TIMES da ta shahara wanen bankado kamayamayar mahukunta a Najeriya da kuma tsage gaskiya komai dacinta.

Dapo, ya kuskure wa fushin gwamnatocin baya da ya kai ga sai da yayi gudun hijra a lokacin mulkin Janar Sani Abacha inda ya samu mafaka a kasar Amurka.

A shekarar 2017, jami’an tsaro na SSS sun tsare Dapo da daya daga cikin wakiliyar jaridar sa saboda wani labarin tonon silili da tsage gaskiya da jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa kan rundunar sojin Najeriya.

Wadannan na daga cikin jajircewar sa da CPJ ta ga cancantar sa na samun kyauta da karramawar ta na 2020.

Sauran wandanda za a karrama sun hada da Svetlana Prokopyeva  daga kasar Rasha

Shahidul Alam  daga kasar Bangladesh sai kuma Mohammad Mosaed daga kasar Iran.

Duka wadannan fitattun ‘yan jarida sun sha wahalar zaman gidajen kaso a dalilin aikin jarida.

Share.

game da Author