Kungiyar Jami’an Kula Da Lafiya ‘JOHESU’ za su tafi yajin aiki

0

Kungiyar Jami’an Kula da Lafiya ta JOHESU, ta yi barazanar daina zuwa aiki a dukkan asibitocin fadin kasar nan, har sai gwamnatin tarayya ta saisaita rashin adalcin da kungiyar ta ce ana nuna wa mambobin ta.

Babban korafin da JOHESU ke yi, shi ne na biyan ta kudaden da ba su wuce a yi kalacin safe da su ba, a matsayin kudaden alawus din jefa kai cikin hatsari da kuma sayar da rayuka da ma’aikata ke yi a yayin gudanar da aikin su.

JOSHESU ta yi barazanar tafiya wannan yajin aiki, mako biyu bayan Kungiyar Likitoci ta Kasa (NARD) ta janye na ta yajin aikin da ta afka sakamakon rike wa mambobin ta albashi da alawus a lokacin nan da suke ta aikin jidalin dakile cutar Coronavirus.

A na ta bangaren, JOHESU ta zargi gwamnatin tarayya da nuna wa mambobin ta wariya, inda ta kara wa likitoci kudaden alawus din shiga hatsari da sayar da rai zuwa kashi 50% na zunzurutun albashin kowane likita.

Wannan kari da aka yi wa likitoci ya tunzura JOSEHU, ta ce duk da mambobin ta BA likitoci ba ne, jami’an kula da marasa lafiya ne, to ai likitoci ba su fi su shiga hatsari ba.

Kafin a yi wa likitoci karin alawus din da a Turance ake kira ‘hazard allowance’, kudin goro ake yi ana bai wa dukkan jami’an asibiti naira 5,000 kacal.

Karin da gwamnatin tarayya ta yi da bai shafi ‘yan JOSEHU ba, ya bata musu rayuka kwarai.

Hakan ta sa suka kira taron manema labarai domin su sanar da gargadin gwamnati cewa za su tafi yajin aiki har sai an biya su hakkokin su.

“An raina mana wayau ne kawai. Ba mu damu ba don albashin mu bai kai na cikakkun likitoci ba. To amma mu jami’an kula da marasa lafiya idan ana maganar kudaden alawus, ai mun fi su shiga hatsari, musamman a lokacin annobar Coronavirus din nan.

“Misali mai wankin kayan majiyyata da goge kayan shimfidu da tufafin marasa lafiya, ai sun fi likitoci shiga hatsari. Amma ya za a ba su alawus cikin-cokali, su Kula likitoci a ba su alawus kashi 50% bisa kashi 100% na zunzurutun albashin su? Wannan ai rashin adalci ne.”

Kungiyar ta ce jami’an kula da marasa lafiya ke fara kai caffa ga majiyyaci a duk halin da ya ke ciki, kafin likita ya zo kan sa.

Idan ba manta ba, kusan jami’an kula da lafiya 1,000 ne suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya, sakamakon cudanya da suke yi tare d masu cutar.

Sun kuma yi kukan rike wa wasun su albashi da aka yi ba tare da an biya su ba. A hakan ne suka ce ba za su daina zuwa aiki har sai an biya su hakkokin su.

Jama’a da dama na mamakin yadda likitoci da jami’an lafiya ke kukan yadda gwamnatin tarayya ke wasa da rayuwar su, a lokacin da su kuma su ke sayar da rayukan su wajen aikin dakile cutar Coronavirus.

Ana mamakin duk da irin makudan milyoyin kudaden da ake kashewa, amma kuma likitoci da jami’an lafiya ke kwana su na tashi da korafe-korafen rashin biyan su hakkokin su.

Share.

game da Author