KUDIN AGAJI: Majalisa za ta binciki ‘yadda Shugaban Hukumar NEDC ya yi daga-daga da naira bilyan 100

0

Majalisar Tarayya ta umarci Kwamitin Harkokin Kudade, Kwangiloli da na NEDC su binciki zargin yadda aka yi daga-daga da naira bilyan 100 cikin shekara daya a kudaden da gwamnatin tarayya ta ware domin a farfado da Yankin Arewa maso Gabas da Boko Haram suka ragargaza.

Wannan bincike ya zo ne kwana jim kadan bayan kammala binciken yadda aka kacaccala sama da naira bilyan 80 a Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta, mai arzikin danyen man fetur.

Shugaban Masu Rinjaye, Ndudi Elumelu ne ya mike ya gabatar da bukatar a binciki yadda aka dagargaje kudade har naira bilyan 100 a Hukumar Farfado da Yankin Arewa maso Gabas (NEDC), wato North East Development Commission a Turance.

Dalin Kafa Hukumar Farfado Da Arewa maso Gabas:

Shugaba Muhammdu Buhari ne ya kafa wannan hukuma domin:

1. A rika mika mata kudade da aljihun gwamnatin tarayya da gudummawa daga kasashen duniya domin farfado da Yankin Arewa maso Gabas (Jihohin Yobe, Barno da Adamawa) da Boko Haram ya ragargaza.

2. Ayyukan wannan hukuma sun hada da:

i. Sake tsugunar da wadanda Boko Haram suka fatattaka ko suka kona wa muhalli.

ii. Gyara muhallan wadanda Boko Haram suka tarwatsa wa gidaje.

iii. Sake ginawa da gyaran tirinan da Boko Haram suka lalata.

iv. Sake gidaje da kantuna da shagunan wadanda Boko Haram suka kassara.

v. Samar da tsare-tsaren kawar da kuncin fatara da talauci a yankin Arewa maso Gabas.

vi. Farfado da darajar ilmin zamani a yankin.

vii. Shawo kan zaizayar kasa da gurbscewar yanayin yankin.

Da kuma wasu ayyuka da suka jibinci ire-iren wadannan da makamantan su.

Zarge-zargen da ake wa Shugaban Hukumar NEDC:

1. Honorabul Elumelu ya ce ana zargin Shugaban Hukumar Farfado Da Arewa Maso Gabas Mohammed Alkali da yin banga-banga shi kadai a kan kudaden hukumar, sai yadda ya ga dama kawai ya ke yi.

2. Ya na kara aringizon makudan kudade a kwangilolin da hukumar ke bayarwa.

3. An bai wa Hukumar NEDC naira bilyan 100, amma an ragargaza kudaden cikin shekara daya, kuma babu wani abu sahihi guda daya da za a iya nunawa a ce an yi da kudaden a Barno, Yobe ko Adamawa.

4. Mohammed Alkali sai jidar kudaden hakkin wadanda Boko Haram suka kassara ya ke yi, ya na sayen kantama-kantaman gidaje a Abuja, Kaduna da Maiduguri.

5. Alkali ya kwashi naira bilyan 5 shi kadai, ba tare da shawara ko neman amincewar Hukumar Kula Da NEDC ba, ya je ya sayo kayan yaki da cutar Coronavirus ya raba.

6. Ya hada baki da Ministar Ayyukan Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Faruq, ya ba ta naira bilyan biyar ta sayo motocin da ta ce ta raba wa sojojin da ke aikin dakile Boko Haram.

Tuni dai hankulan jama’a suka karkato a kan wannan zargin badakala domin a ga yadda ‘yan ‘boko halal’ suka jide kudaden tallafin wadanda ‘yan Boko Haram suka kassara.

Share.

game da Author