Kotu ta kwato maka-makan gidaje 48 a hannun tsohuwar Shugabar Hukumar NSITF

0

Mai Shari’a Taiwo Taiwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya bada umarnin EFCC ta kwace wasu maka-makan kadarori har 48 daga hannun tsohuwar Shugabar Hukumar NSITF, Ngozi Olejeme.

Taiwo ya yanke wannan hukunci ne a ranar Larabar nan, a Abuja, mako guda bayan ya yanke hukuncin cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta biya iyalan wasu ‘yan Shi’a uku da ‘yan sanda suka bindige, naira milyan 15, tare da mika gawarwakin su ga iyalan.

Maka-makan gine-ginen da za a kwace daga hannun ta su na Abuja, Bayelsa, Enugu, Edo da Delta.

Olejeme wadda ita ce ma’ajin kudaden kamfe din Jonathan-Sambo a 2015, ta tsere daga Najeriya tun cikin 2016, bayan da jami’an Hukumar EFCC su ka kada kararrawar cigiyar damke ta, bisa zargin ta da wani Umar Abubakar da laifin yin wasan-kura da naira bilyan 69 na hukumar.

Abubakar shi ma tsohon Shugaban Hukumar NSITF din ne.

An zargi sun rika karkatar da kudaden zuwa aljifan su ta hanyar bai wa kamfanonin su kwangiloli a asirce.

Wani gazagurun magulmaci ne ya kyankyasa wa EFCC bayanan irin makudan kudaden da su Olejeme su ka sata.

Mai Shari’a Taiwo ya bada umarnin kwace gidajen bayan bayan da lauyan EFCC ya gabatar masa da hujjojin da ke nuna cewa da kudaden sata Olejeme ta yi gidajen.

Sai dai ya umarci EFCC kuma ta buga bayanan cewa ta kwace gidajen daga hannun matar a shafukan jaridun kasar nan nan da mako daya.

Ya ce wa EFCC ta buga cewa ta kwace gidan, amma idan akwai mai jayayya cewa na sa ne, to ya garzaya kotu cikin makonni biyu.

Taiwo ya ce za a ci gaba sa saurare a kotu ranar 27 Ga Yuli, 2020.

Share.

game da Author