A ranar Alhamis ne kotu a Mararaba, jihar Nasarawa ta yi watsi da Karar da wata Mata Mai suna Deborah Joseph ta shigar ta na neman kotu ta raba auren ta da mijinta Joseph.
Deborah ta koka cewa mijinta Joseph baya kula da ita yadda ya kamata a tsawon shekaru 10 da suka yi tare.
Deborah ta ce a duk rana Joseph sai ya yi mankas da da giya yake dawo mata gida sannan kuma a can cikin dare.
“Joseph baya kula da iyalensa domin ni ce ke biyan kudin haya, sutura da abincin da ake ci a gidan da muke zaune.
Deborah ta kuma zargi Joseph da kokarin yin amfani da babban dan su don yayi asiri da shi ya samu kudi.
Joseph ya musanta duk abinda matarsa Deborah ta fadi a kotu.
Ya ce yana son matarsa da ‘ya’yan sa biyu.
Joseph ya ce soyayyar dake tsakaninsa da Deborah ya sauya salo ne tun da aka kore shi daga aiki, daga nan ne ta canja masa.
Ya roki kotu ta yi watsi da butatar Debora na a raba auren, cewa yana son matar sa har yanzu.
Alkalin kotun Ibrahim Shekarau ya umurci ma’auratan su koma gida su sassanta kansu.
Za a ci gaba da Shari’a ranar 12 ga watan Agusta.
Discussion about this post