Kotu ta daure mahaifin da ya yi wa ‘ya’yan sa mata biyu fyade

0

Babban kotu dake garin Ado Ekiti jihar Ekiti ta yanke wa mahaifin wasu ‘yan mata biyu da ya rika lalata da su mai suna Imole Akintewe dake da shekaru 65 a duniya hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekara biyar bayan ta kama shi da laifin yi wa ‘ya’yansa Mata biyu fyade.

Alkalin kotun John Adeyeye ya ce ya yanke wa Akintewe wannan hukunci ne saboda tsawon shekaru da take dashi da rokon sassauci da yi.

Alkalin Adeyeye ya ce Akintewe zai yi zaman gidan kaso ba tare da beli ba na tsawon shekaru 5.

A lokacin zaman kotun, lauyan da ya shigar da karar Felix Awoniyi, ya bayyana cewa Akintewe ya aikata wannan laifi ne ranar 28 ga Mayun 2019.

“Bincike ya nuna cewa Akintewe ya fara lalata da ‘ya’yan sa mata biyu masu shekaru 9 da 13 bayan matarsa Kuma mahaifiyarsu ta rasu.

“Tun bayan wannan lokaci Akintewe ya rika lalata da ‘ya’yansa Kamar matan shi.

Awoniyi ya gabatar da shaidu guda bakwai Wanda a ciki akwai likita da jami’in tsaro da suka tabbatar da aika-aikan da Akintewe ya aikata.

Idan ba a manta ba a ranar 14 ga watan Yuli kotun majistare dake jihar Kano ta daure Umar Abdulrahman mai shekaru 34 a kurkuku na tsawon watanni 24 bayan ta kama shi da laifin cin zarafin yara kanana maza ta baya.

Alkalin kotun Muhammed Idris ya ce Abdulrahman zai yi zaman kurkuku ba tare da beli ba.

Lauyan da ya shigar da karar Badamasi Gawuna ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama Abdulrahman bayan Umar Tanko da Ahmed Bello iyayen wadannan yara kuma mazaunan kwatas din Mundadu sun kawo kara ofishin ‘yan sanda dake unguwar Kumbotoso ranar 23 ga watan Afrilu.

Share.

game da Author