Kotu ta daure birkilan da ya yi wa ‘yar shekara 16 fyade

0

A ranar Litini kotun majistare dake Iyaganku, jihar Oyo ta daure wani birkila da ta kama da laifin yi wa ‘yar shekara 16 fyade a jihar.

Alkaline kotun Titilayo Oyekanmi ta ce birkilan mai suna Sodiq Raifu zai yi zaman kurkuku har sai kotu ta kammala shawara da fannin ofishin ‘yan sandan dake bincikar irin wadanna laifuka.

Oyekanmi ta Yanke wannan hukunci ne bayan watsi da rokon sassauci da Raifu ya yi.

Za a ci gaba da shari’an ranar 5 ga watan Oktoba.

A zaman kotun lauyan da ya shigar da karar Sunday Ojeleye ya ce Rafiu ya yi lalata da wannan yarinya da misalin karfe bakwai na daren ranar 27 ga watan Yuni.

“Rafiu dake zaune a unguwar Akobo a garin Ibadan ya dade ya yi fakon wannan yarinya dake hanyar dawowa gida daga wajen talla inda da ta shiga wani lungu sai ya bita ya danne ta.

Ojeleye ya ce mahaifin yarinyar ne ya kawo kara ofishin ‘yan sandan dake Akobo.

Idan ba a manta ba a cikin makon da ya gabata Jam’ian rundunar Sibul Difens a Kaduna sun damke wani limamin Cocin ,Faith Agape dake Unguwar Narayi, a Kaduna mai suna , Joseph Alhassan, bayan an zarge sa da yin lalata da ‘yar aikin sa na tsawon shekara 5.

Wannan yarinya dai wanda ‘yar asalin karamar hukumar Kagarko, tuni har iyayen ta sun tafi da ita bayan samun labarin abinda ya faru tsakanin ta da fasto Alhassan.

Shi ko Fasto Alhassan, wanda dan Asalin Karamar hukumar Lere ne, garin Saminaka ya karyata wannan zargi, inda ya ce shi kazafi aka yi masa amma abinda ake zargin sa da shi babu kamshin gaskiya a ciki.

Share.

game da Author