Kotu a Kano ta daure Umar da yaci zarafin yara maza uku ya biya su naira Hamsin-Hamsin

0

A ranar Talata, kotun majistare dake jihar Kano ta daure Umar Abdulrahman mai shekaru 34 a kurkuku na tsawon watanni 24 bayan ta kama shi da laifin cin zarafin yara kanana maza ta baya.

Alkalin kotun Muhammed Idris ya ce Abdulrahman zai yi zaman kurkuku ba tare da beli ba.

Lauyan da ya shigar da karar Badamasi Gawuna ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama Abdulrahman bayan Umar Tanko da Ahmed Bello iyayen wadannan yara kuma mazaunan kwatas din Mundadu sun kawo kara ofishin ‘yan sanda dake unguwar Kumbotoso ranar 23 ga watan Afrilu.

Iyayen sun bayyana cewa a cikin watan Afrilu ne Abdulrahman dake Zama a kwatas din Layin Yankifi Maidile ya san yadda yayi ya rudi wadannan yara uku zuwa dakinsa inda ya Yi lalata da su sannan ya biya kowanen su Naira 50 kudin sallama.

Share.

game da Author