Korona ta yi ajalin Kwamishinan lafiyar jihar Ondo

0

Kwana daya cur bayan gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bayyana kamuwa da cutar Korona da yayi, kwamishinan lafiyar jihar Wahab Adegbenro,ya rasu a dalilin kamuwa da kwayoyin cutar.

Wahab Adegbenro ya rasu da safiyar Alhamis.

Haka kuma gwamna Akeredolu ya umarci duka manyan ma’aikatan gwamnati da su gaggauta yin gwajin cutar sannan su killace kan su.

Majiya ta ce ya rasu a asibitin da ake kula da masu fama da kwayoyin cuta na jihar.

Duk da dai gwamnati bata fadi kai tsaye cutar da tayi ajalin sa ba, kwararan majiya sun shaida cewa Korona ce ta yi ajalin sa.

A jihar Delta ma gwamnan jihar Ifeanyi Okowa da mai dakin sa duk sun killace kansu bayan tabbatar muce da suna dauke da cutar Korona din.

Share.

game da Author