Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa ta sallami fursunoni 8,713 a fadin kasar nan, saboda fargabar fantsamar cutar Coronavirus a cikin gidajen kurkukun kasar nan.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana haka a wani taro a Abuja ranar Talata.
Taron dai Kwamitin Shugaban Kasa Kan Rage Cinkoson Kurkuku Da Yi Wa Daurarru Afuwa ne ya shirya shi, domin su yi bitar nasarorin da suka samu tun daga lokacin kafa kwamitin, cikin 2017 zuwa Kano yau.
“Mun yi zagayen duba-garin gidajen kurkukun kasar nan har 39 a cikin jihohi 18.
“Ina sanar da cewa kwamitin mu ya sallami daurarru 8,713 a cikin wadannan jihohi 18.
“Shugaban Kasa ne ya nemi a rage cinkoson daurarru gudun kada Coronavirus ta fantsama a gidajen kurkuku ta yi mummunan illa.
“Sannan kuma a zagayen da wannan kwamiti ya yi, ya lura cinkoson daurarru a gidajen kurkuku sun nunka adadin ka’idar yawan wadanda za a tsare kusan sau uku.
“Domin rage cinkoso, Gwamnatin Tarayya na kan aikin gina kurkuku mai daukar mutum 3,000 a Karshi, Abuja da wani mai cin mutum 3,000 a Janguza, Kano.
Shugaban Kwamitin kuma Babban Jinin Kotun Majistare na Kasa, Ishaq Bello, ya kara da cewa sallamar daurarrun ya rage wahalhalun kashe kudade da dawainiyar yi musu gwaji.
Ya ce kwamitin ya bai wa gwamnati shawarar yadda za a gyara gidajen kurkuku a kasar nan, ganin cewa yawancin gidajen kurkukun da suka ziyarta, sun lalace matuka.