Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 460 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum-150, Rivers-49, Oyo-43, Delta-38, FCT-26, Anambra-20, Kano-20 Filato -18, Edo-14, Bayelsa-13, Enugu-13, Osun-12, Kwara-10, Borno-8, Ogun-7,Kaduna-6, Imo-4, Bauchi-3, Gombe-3, Niger-2 da Adamawa-1
Yanzu mutum 30,249 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 12,373 sun warke, 684 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 17,192 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum,11,670 daga nan sai FCT – 2,348 , Oyo – 1,573, Edo – 1,503, Kano – 1,291, Delta – 1,323, Rivers – 1,284, Ogun – 1,057, Kaduna – 889, Katsina 628, Borno – 563, Bauchi – 519, Gombe – 524, Ebonyi – 503, Filato – 478, Ondo – 550, Abia – 400, Enugu – 431, Imo – 356, Jigawa – 318, Kwara – 307, Bayelsa – 282, Nasarawa – 234, Osun – 210, Sokoto – 153, Niger – 124, Akwa Ibom – 112, Benue – 121, Adamawa – 100, Kebbi – 86, Zamfara – 76, Anambra – 93, Yobe – 61, Ekiti – 45, Taraba – 27, Kogi – 5 da Cross Rivers – 5.
Wasu abinci da ke kara karfin garkuwar jiki:
Wasu kwararrun likitoci daga kasar UK sun shaida cewa sinadarin ‘Vitamin D’ baya warkar da cutar coronavirus.
Likitoci sun fadi haka ne ganin yadda wasu mutane ke fadin cewa sinadarin ‘Vitamin D’ na da ingancin warkar da cutar coronavirus.
Sinadarin ‘Vitamin D’ na kara karfin kashi, inganta karfin garkuwan jiki sannan yana kare mutum daga kamuwa da cututtukan dake sa a samu matsalar toshewar numfashi, kuma wara na da wannan sanadari.
A dalilin haka likitoci ke Kira ga mutane da su rika cin abinci dake dauke da sinadarin ‘Vitamin D’ domin inganta garkuwar jikinsu amma ba domin su kare kansu daga kamuwa da cutar coronavirus ba.
Abincin dake dauke da sinadarin Vitamin D sun hada da:
1. Dafaffen kwai
2. Lemun Zaki
3. Hanta dafaffe ko Kuma soyayye
4. Kifi
5. Madara
6. Madaran waken soya
7. Wara
8. Kubewa
Discussion about this post