Kungiyar likitocin jihar Legas karkashin ‘Medical Guild’ ta yi barazanar daina zuwa aiki a duk asibitocin da ake kula da masu fama da cutar coronavirus a jihar na tsawon kwanaki uku har Sai gwamnati ta biya musu bukatunsu.
Shugaban kungiyar Oluwajimi Sodipo ya Sanar da haka wa manema labarai ranar Lahadi, yana mai cewa kungiyar za ta fara yajin aikin somin tabi daga ranar 13 zuwa 16 ga watan Yuli.
Sodipo ya ce bukatun kungiyar sun hada da rashin biyan Likitoci albashin su na tsawon watanni biyu, banbanta albashin Likitocin dake aiki da gwamnati jihar da na gwamnati tarayya, rashin biyan su alawus, rashin Samar da isassun kayan Samun kariya daga Korona, rashin inshorar lafiya wa ma’aikata da rashin isassun likitoci a asibitocin gwamnati a jihar.
Ya ce a dalilin wadannan matsaloli kungiyar ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 21 domin ta biya bukatunsu inda a ranar 27 ga watan Yuni wadannan kwanaki suka cika, kuma ta kara wa gwamnati kwanaki 14.
Sodipo ya ce kungiyar za ta zauna bayan wa’adin kwanaki ukun da ta bada sun cika domin tattauna matakin da za su dauka a gaba.
Medical Guild’ kungiya ce ta Likitocin dake aiki da gwamnati jihar Legas.
Idan ba a manta ba a ranar 1 ga watan Yuli Kungiyar ma’aikatan Kula da Lafiya ta JOHESU, ta yi barazanar daina zuwa aiki a dukkan asibitocin fadin kasar nan, har sai gwamnatin tarayya ta saisaita rashin adalcin da kungiyar ta ce ana nuna wa mambobin ta.
Babban korafin da JOHESU ke yi, shi ne na biyan ta kudaden da ba su wuce a yi kalacin safe da su ba, a matsayin kudaden alawus din jefa kai cikin hatsari da kuma sayar da rayuka da ma’aikata ke yi a yayin gudanar da aikin su.
JOSHESU ta yi barazanar tafiya wannan yajin aiki, mako biyu bayan Kungiyar Likitoci ta Kasa (NARD) ta janye na ta yajin aikin da ta afka sakamakon rike wa mambobin ta albashi da alawus a lokacin nan da suke ta aikin jidalin dakile cutar Coronavirus.
Discussion about this post