Kwamishinan al’adun gargajiya da yada labarai na jihar Nasarawa, Dogo Shammah ya bayyana cewa gwamnati ta umurci duk kwamishinonin jihar da su killace kansu na tsawon kwanakin 14 domin guje wa kamuwa da cutar Covid-19.
Shammah ya ce haka ya biyo bayan kamuwa da cutar da kwamishinan Shari’a kuma Atoni-Janar din jihar Abdulkareem Kana ya yi.
Ya ce kwamishinonin za su killace Kan su daga ranar Juma’a bayan an dauki jininsu sannan su fito bayan sakamakon gwajin ya fito.
Gwamnan jihar Abdullahi Sule ya Sanar da haka a zaman da kwamitin zartaswar jihar ranar 3 ga watan Yuli.
Shammah ya yi Kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharruddan gujewa kamuwa da cutar domin Kare kansu.
Bayan haka kwamishinan Shari’a Abdulkareem Kana a hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis ya bayyana cewa tun a makon da ta gabata ne ya fara fama da mura inda daga nan ya fara samun alamun zazzabi, zafi a makogoro, yoyon hanci, jin gajiya da dai sauran su.
Kana ya ce likitoci sun hada masa maganin zazzabin cizon sauro da Vitamin C yana Sha.
“Da na fara shan maganin sai na ji sauki Amma duk da haka na kira hukumar NCDC domin a yi mun gwajin cutar coronavirus.
“Sakamakon gwajin cutar ya nuna na kamu sannan a yanzu haka Ina killace a gida Kuma Ina samun sauki.
A yanzu mutum 236 ne Suka kami da cutar a jihar Nasarawa.
Daga ciki 115 na kwance a asibiti, an sallami 113 sannan 8 sun mutu.
Discussion about this post