KORONA: Kwamishinan yada labarai da wasu Mutum 21 sun warke a jihar Delta

0

A ranar Talata gwamnatin jihar Delta ta bayyana cewa an sallami kwamishinan yada labarai na jihar Charles Aniagwu da wasu mutane 21 da suka kamu da cutar coronavirus bayan sun yi kwanakin 17 a wurin killace masu fama da cutar.

Sakataren yada labaran gwamnan jihar, Olisa Ifeajika ya Sanar da haka wa manema labarai a garin Asaba.

Ifeajika ya ce an sallami wadannan mutane bayan sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna cewa basu dauke da cutar.

Ya ce tun a ranar 20 ga watan Yuni sakamakon gwajin Charles Aniagwu ya nuna cewa ya warke daga cutar.

Bayan haka Ifeajika ya ce sakataren gwamnatin jihar Chiedu Ebie Wanda ya kamu da cutar tare da Charles Aniagwu na killace a asibiti saboda har yanzu sakamakon gwajin cutar da aka Yi masa domin tabbatar cewa ya warke bai fito ba.

Idan ba a manta ba a ranar 21 ga watan Yuni aka bayyana kamuwa da cutar da sakataren gwamnatin jihar Chiedu Ebie da kwamishinan yada labarai na jihar Charles Aniagwu suka yi.

A dalilin haka gwamnati ta yi kira ga mutanen jihar da su kiyaye sharuddan gujewa wa kamuwa da cutar.

Gwamnati ta yi Kira ga mutanen jihar da su cigaba da kiyaye wa da bin sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin Kare lafiyar su.

Yanzu mutum 1,285 ne suka kamu a jihar, mutum 853 na kwance a asibiti, an sallami mutum 408, murum 25 sun mutu.

Share.

game da Author