KORONA: Jiha za ta fara cin tarar wanda bai saka takunkumin fuska ba

0

Gwamnatin jihar Ekiti ta ce daga ranar Litini za a fara hukunta duk wanda ya karya dokar Korona a jihar.

Atoni-janar Kuma kwamishinan Shari’a na jihar Wale Fapounda ya Sanar da haka wa manema labarai a garin Ado-Ekiti.

Fapounda ya ce daga yanzu gwamnati za ta tilasta amfani da takunkumin fuska musamman idan za a fita ko kuma idan ana cikin taron mutane saboda dakile yaduwar cutar Covid-19 a jihar.

Kwamishinan Shari’ a ya ce daga yanzu gwamnati ba zata yi kasa-kasa ba wajen hukunta duk wanda aka kama ya karya dokokin Korona a jihar.

Bisa ga sakamakon gwajin cutar da hukumar NCDC ta gabatar ranar Litini ya nuna cewa mutum 86 ne suka kamu da cutar a jihar inda daga ciki 37 na kwance a asibiti.

An sallami 47 sannan biyu sun mutu a jihar.

Sakamakon ya Kuma nuna cewa mutum 37,225 ne suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 15,333 sun warke, 801 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 21,091 ke dauke da cutar a Najeriya.

Share.

game da Author