KORONA: Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta janye dokar hana taron aure da Jana’iza a jihar

0

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta janye dokar hana taron aure da Jana’iza da ta saka a jihar tun a watan Maris domin dakile yaduwar cutar Korona a jihar.

Gwamnan jihar Emmanuel Udom ya Sanar da haka ranar Alhamis yana mai cewa yanzu mutane za su iya gudanar da tarukkan aure da Jana’iza a jihar amma za a yi haka ne bisa ga sharuddan gujewa kamuwa da cutar da kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta amince da su.

“Idan za a yi taron Jana’iza a fili kada a taru ya wuce mutum 50.

“Idan Kuma za a yi taron a cikin coci ne taron mutane kada ya wuce mutum 30. Sannan kuma kowa zai saka takunkumin fuska da yin nesa-nesa da juna.

Udom ya ce gwamnati za ta yi saka jami’an tsaro domin tabbatar da kowa ya bi doka.

Gwamnan Udom ya kuma yi kira ga malaman addini da su hadda hannu da gwamnati domin ganin mutane sun kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar.

“Muna Kira ga mutane da su juri amfani da takunkumin fuska sannan idan mutum ya ga ba zai iya ba ya zauna kawai a gida.

“Kula da Mai dauke da cutar covid-19 na da tsada saboda rashin magani sannan a yanzu haka ko kobo ban karba ba daga gwamnati tarayya.

Mutum 104 ne suka kamu, 48 na asibiti, 54 sun warke sannan 2 sun mutu a jihar.

Share.

game da Author