Gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola ya garkame wasu kananan hukumomi hudu a jihar a dalilin bullar cutar Korona.
Gwamnati ta yi haka ganin yadda cutar ta fantsama wadannan kananan hukumomi kamar wutan dare.
Kananan hukumomi da gwamnati ta garkame sun hada da Ilesa ta Gabas, Ilesa ta Yamma, Atakumosa ta Gabas da Atakumosa ta Yamma.
Kwamishinan yada labarai Funke Egbemode ta Sanar da haka a wata takarda da aka rabawa manema labarai ranar Asabar.
Funke ta ce dokar zaman gida dole da gwamnati ta saka a wadannan kananan hukumomi zai Fara aiki ranar 7 ga watan Yuli sannan na tsawon mako daya.
Gwamnati ta ce ma’aikatan gidan jarida, ma’aikatan kiwon lafiya, ma’aikatan hukumar gobara da sauran su be kadai za su rika zuwa aiki daga wadannan kananan hukumomi.
“Idan ba a manta ba a cikin kwanakin nan ne gwamnatin tarayya ta janye dokar hana tafiye-tafiye wanda a dole muma muka janye dokar zaman gida dole a duk fadin jihar banda wadannan kananan hukumomi hudu.
“Duk da haka gwamnati ta saka dokar hana walwala daga karfe 5 na safe zuwa 9 na dare sannan jami’an tsaro zasu hukunta duk wanda ya karya dokar.
“Gwamnati ta ce ta bude gidajen ibadu sannan za su gudanar da aiyukan su bisa ga sharuddan guje wa kamuwa da cutar da ke jihar.
“Kananan hukumomi hudu da gwamnati ta garkame za su kiyaye dokar zaman gida dole a aka saka tare da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar da hukumar NCDC ta saka.
Gwamnati ta yi kira ga mazauna wadannan kananan hukumomi da su fito su yi cefanen kayan abinci.
Mutum 151 ne suka kamu da cutar a jihar daga ciki 87 na kwance a asibiti, an sallami 59 sannan biyar sun mutu.
Discussion about this post