KORONA: Dole ka saka Takunkumin Fuska idan ka shiga jama’a a Kano -Inji Ganduje

0

Gwamnatin jihar Kano ta raba wa kungiyoyi takunkumin fuska guda miliyan biyu domin dalike yaduwar cutar Korona a jihar.

Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya raba takunkumin ranar Lahadi ga kungiyoyin ‘yan kasuwa, dalibai, NARTO, NURTW da sharadin cewa za su jajirce wajen amfani da su.

Gwamna Ganduje ya kuma saka dokar sa takunkumin fuska dole musamman a lokacin da mutum zai gwamatsu cikin jama’a jihar.

“Gwamnati na kokarin ganin an samu dawwamammiyar hanyar dakile yaduwar cutar Covid-19 a jihar da hakan ya zama dole mutane su kiyaye dokoki da sharuddan gujewa kamuwa da cutar.

” Mutane a jihar basu kaunar saka takunkumin fuska musamman idan suna cikin jama’a. Daga yanzu gwamnati ta umarci Jami’an tsaro domin tilasta wa mutane suna saka takunkumin fuska dole.

Gwamnati ta yi Kira ga kungiyoyin NARTO NURTW da su rika amfani da takunkumin fuska sannan direbobi su tabbatar duk fasinjar da zasu dauka ya saka takunkumin.

Bayan haka mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna ya ce kwanakin baya gwamnati ta raba takunkumin fuska miliyan uku ga kungiyoyi a jihar domin hana yaduwar cutar.

Gawuna ya Yi Kira ga mutane da su hada hannu da gwamnati domin ganin an dakile yaduwar cutar Covid-19 a jihar.

Mai martaba sarkin Kano Aminu Bayero ya Yi Kira ga mutane da su kiyaye sharudda da dokokin gujewa kamuwa da cutar da gwamnati ta saka musamman a lokacin shagulgular babban Sallah.

Share.

game da Author