Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 664 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -224, FCT-105, Edo-85, Ondo-64, Kaduna-32, Imo-27, Osun-19, Filato-17, Oyo-17, Ogun-17, Rivers-14, Delta-11, Adamawa-10, Enugu-7, Nassarawa-6, Gombe-3, Abia-3 da Ekiti-3.
Yanzu mutum 31987 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 13,103 sun warke, 724 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 18,160 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum12,275, FCT – 2,538, Oyo – 1,706, Edo – 1, 678, Delta – 1,359, Rivers – 1,357, Kano – 1,303, Ogun – 1,080, Kaduna – 978, Katsina – 665, Ondo – 670, Borno – 586, Gombe – 530, Bauchi – 519, Ebonyi – 508, Filato – 516, Enugu – 476, Abia – 405, Imo – 386, Jigawa – 321, Kwara – 311, Bayelsa – 299, Nasarawa – 244, Osun – 231, Sokoto – 153, Niger – 135, Akwa Ibom – 134, Benue – 121, Adamawa – 110, Anambra – 93, Kebbi – 86, Zamfara – 76, Yobe – 62, Ekiti – 49, Taraba- 27, Kogi – 5, da Cross River – 5.
Wasu abinci da ke kara karfin garkuwar jiki:
Wasu kwararrun likitoci dake a kasar UK sun shaida cewa sinadarin ‘Vitamin D’ baya warkar da cutar coronavirus.
Likitoci sun fadi haka ne ganin yadda wasu mutane ke fadin cewa sinadarin ‘Vitamin D’ na da ingancin warkar da cutar coronavirus.
Sinadarin ‘Vitamin D’ na kara karfin kashi, inganta karfin garkuwan jiki sannan yana kare mutum daga kamuwa da cututtukan dake sa a samu matsalar toshewar numfashi, kuma wara na da wannan sanadari.
A dalilin haka likitoci ke Kira ga mutane da su rika cin abinci dake dauke da sinadarin ‘Vitamin D’ domin inganta garkuwar jikinsu amma ba domin su kare kansu daga kamuwa da cutar coronavirus ba.
Abincin dake dauke da sinadarin Vitamin D sun hada da:
1. Dafaffen kwai
2. Lemun Zaki
3. Hanta dafaffe ko Kuma soyayye
4. Kifi
5. Madara
6. Madaran waken soya
7. Wara
8. Kubewa
Discussion about this post