Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 595 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 156, Oyo-141,FCT-99, Edo-47, Kaduna-27, Ondo-22, Rivers-20, Osun-17, Imo-13, Filato-10, Nasarawa-8, Anambra-8, Kano-5, Benue-5, Borno-5, Ogun-4, Taraba-3, Gombe-3, Kebbi-1 da Cross Rivers-1.
Yanzu mutum 33,153 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 13, 671 sun warke, 744 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 18,738 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 12,583, FCT – 2,675, Oyo – 1,867, Edo – 1,778, Delta – 1,359, Rivers – 1,388, Kano – 1,314, Ogun – 1,091, Kaduna – 1,016, Katsina – 1,726, Ondo – 738, Borno – 591, Gombe – 533, Bauchi – 521, Ebonyi – 616, Filato – 543, Enugu – 476, Abia – 405, Imo – 399, Jigawa – 321, Kwara – 330, Bayelsa – 313, Nasarawa – 252, Osun – 262, Sokoto – 153, Niger – 145, Akwa Ibom – 145, Benue – 126, Adamawa – 110, Anambra – 101, Kebbi – 87, Zamfara – 76, Yobe – 62, Ekiti – 63, Taraba- 30, Kogi – 5, da Cross River – 10.
Hukumar UNODC dake karkashin majalisar dinkin duniya ta gargadi mutanen kasashen duniya da gwamnatoci, su rika sara suna duban bakin gatari da kuma jan kunnen mutane game da nisanta daga yin mua’mula da tsuntsaye da namun daji.
Rahotan ya nuna cewa Kashi 75 bisa 100 na cututtukan da ake fama da su a duniya na da alaka da cin namun daji.
Rahoton ya kuma nuna cewa cutar SARS-CoV-2 Wanda ya haifar da cutar coronavirus na da alaka da wata dabban daji mai suna pangolins
Shugaban UNODC Ghada Waly, kwamishinan EU Jutta Urpilainen da shugaban ‘Convention on International Trade in Endangered Species of Wild Fauna and Flora (CITES)’ Ivonne Higuero sun yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukan matakan da za su taimaka wajen hana farautar namun daji domin kare muhalli, dabbobin daji da kiwon lafiyar mutane a duniya.