Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 591 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –168, Oyo 191, FCT 61, Ondo 29, Osun 26, Ebonyi 24, Edo 23, Ogun 14, Rivers 13, Akwa Ibom 12, Kaduna 10, Katsina 6, Borno 4, Ekiti 3, Delta 3, Imo 3, Niger 1.
Yanzu mutum 39539 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 16,559 sun warke, 845 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,135 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 14,177 FCT – 3,437, Oyo – 2,497, Edo – 2,128, Delta – 1,456, Rivers –1,600, Kano –1,452, Ogun – 1,241, Kaduna – 1,299, Katsina –723, Ondo – 1,030 , Borno –609, Gombe – 558, Bauchi – 535, Ebonyi – 748, Filato – 780, Enugu – 726, Abia – 527, Imo – 465, Jigawa – 322, Kwara – 707, Bayelsa – 326, Nasarawa – 292, Osun – 420, Sokoto – 153, Niger – 167, Akwa Ibom – 208, Benue – 294, Adamawa – 115, Anambra – 132, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 64, Ekiti – 91, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 34.
Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar covid-19
Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.
Shi cutar akan kama shi ne a dalilin cudanya da dabbobi domin sune ke dauke da ita. Sakamakon bincike da aka yi game da cutar ya nuna cewa akan kamu da cutar ne ta hanyar yin muamula da dabbobi na gida da na daji.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.
Haka kuma idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.
1. A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu
2. Za a iya amfani da man tsaftace hannu wato ‘Hand sanitizer’ domin tsaftace hannu idan Babu riwa da sabulu
3. A rika rufe hanci da baki idan za ayi atishawa kuma tari
4. Wanke da dafa nama sosai ya nuna tubus kafin a ci da kwai
5. Nisanta ko kuma zama kusa da wanda ya nuna alamun rashin lafiya musamman Kira ko Kuma tari
6. A Rika amfani da takunkumin fuska musamman idan za a fita ko Kuma ana cikin mutane
7. A gaggauta zuwa asibiti da neman magani idan ba a da lafiya
Discussion about this post