KORONA: An bude wuraren yin gwajin cutar 59 a Najeriya – NCDC

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa gwamnati ta bude wuraren yin gwajin cutar Korona 59 a jihohi 29 da Abuja.

Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu wanda ya sanar da haka a makon da ya gabata a taron da kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Korona ke yi da manema labarai.

Ihekweazu ya ce hukumar na kokarin ganin an bude wuraren yin gwajin Korona a sauran jihohin da suka rage ba a bude ba.

Ya ce a yanzu haka ma’aikatan hukumar sun maida hankali wajen ganin an kammala bude wuraren gwajin a jihohin Zamfara, Kebbi, Gombe, da Taraba.

Hukumar ta ce yin haka zai taimaka wajen kara yawan yi wa mutane gwajin cutar wanda hakan zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

Idan ba a manta ba sakamakon gwajin cutar da NCDC ta fitar ranar Lahadi ya nuna cewa an samu karin mutum 438 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -156, Kano 65, Ogun 57, Filato 54, Oyo 53, Benue 43, FCT 30, Ondo 18, Kaduna 16, Akwa Ibom 13, Gombe 13, Rivers 12, Ekiti 9, Osun 8, Cross River 3, Borno 2, Edo 2, Bayelsa 1

Yanzu mutum 40532 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 17,374 sun warke, 858 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,300 ke dauke da cutar a Najeriya.

Sannan a duniya kuma mutum miliyan 16 ne suka kamu da cutar, 650,000 sun mutu.

Share.

game da Author