KORONA: Abuja 73, Kaduna 20, Kano 2, yanzu mutum 28, 167 suka kamu a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 603 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Asabar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -135, Edo – 87, FCT – 73, Rivers – 67, Delta – 62, Ogun – 47, Kaduna – 20, Plateau – 19, Osun – 17, Ondo – 16, Enugu – 15, Oyo – 15, Borno – 13, Niger – 6, Nasarawa – 4, Kebbi – 3, Kano – 2, Sokoto – 1 da Abia – 1.

Yanzu mutum 28, 167 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 11, 462 sun warke, 616 sun rasu. Zuwa yanzu mutum 16, 071 ke dauke da cutar a Najeriya

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 11, 045 cases, followed by FCT – 2,153, Oyo – 1,466, Edo – 1,353, Kano – 1,264, Delta – 1,227, Rivers – 1,181, Ogun – 974, Kaduna – 855, Katsina 579, Borno – 528, Bauchi – 516, Gombe – 513, Ebonyi – 438, Plateau – 421, Ondo – 410, Abia – 383, Enugu – 372, Imo – 352, Jigawa – 318, Kwara – 269, Bayelsa – 234, Nasarawa – 225, Osun – 165, Sokoto – 153, Niger – 122, Akwa Ibom – 104, Benue – 97, Adamawa – 89, Kebbi – 84, Zamfara – 76, Anambra – 73, Yobe – 61, Ekiti – 43, Taraba – 19, da Kogi – 5.

Idan ba a manta ba, a ranar Talata, kungiyar kiwon Lafiya ta duniya (WHO), ta bayyana cewa yanzu ne duniya za ta afka cikin babban bala’in Coronavirus.

Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya fitar ya ce a baya ba a ga komai ba tukunna.

Tedros wanda aka buga bayanin sa a BBC da rumbun tattara bayanan kamuwa da kisan adadin mutane sakamakon Coronavirus, wato worldometers.org suka wallafa, ya ce matsawar gwamnatocin kasashen duniya ba su gaggauta tashi tsaye sun yi da gaske ba, to wannan cuta za ta yi wa duniya rundugun da ya wuce wanda ake ciki a yanzu fiye da kima.

Share.

game da Author