Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 563 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –100, FCT-102, Filato-52, Kwara-50, Abia-47, Kaduna-35, Benue-34, Oyo-26, Ebonyi-24, Kano-16, Niger-15, Anambra-14, Gombe-12, Edo-11, Rivers-6, Nasarawa-5, Delta-5, Borno-3, Enugu- 2, Bauchi-2 da Kebbi- 1.
Yanzu mutum 37,225 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 15333 sun warke, 801 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 21,091 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 13,538 FCT – 3,129, Oyo – 2,193, Edo – 2,000, Delta – 1,428, Rivers – 1,535, Kano –1,416, Ogun – 1,174, Kaduna – 1,191, Katsina –710, Ondo – 925 , Borno –602, Gombe – 558, Bauchi – 531, Ebonyi – 679, Filato – 700, Enugu – 677, Abia – 526, Imo – 452, Jigawa – 322, Kwara – 585, Bayelsa – 322, Nasarawa – 281, Osun – 351, Sokoto – 153, Niger – 166, Akwa Ibom – 175, Benue – 294, Adamawa – 115, Anambra – 132, Kebbi – 89, Zamfara – 77, Yobe – 64, Ekiti – 86, Taraba- 30, Kogi – 5, da Cross Rivers – 13.
Matakan da Zamfara ta dauka wajen dakile yaduwar Korona a jihar
Kakakin gwamnan jihar, Zailani Bappa ya bayyana matakan da gwamnatin jihar ta dauka da ya sa aka samu nasarar dakile yaduwar cutar a jihar.
1 – Gwamnati Zamfara ta bi dokar gwamnatin tarayya sauda kafa tun da farkon bullowar cutar a kasar nan.
Mun rufe makarantun mu tunda wuri, mun rufe kasuwanni da iyakokin jihar mu, sannan mun saka dokar kowa ya saka takunkumin fuska dole-dole. Mun yi haka ne tun kadin cutar ta dira jihar mu ma.
2 – Kafin cutar ta bulla a Zamfara gwamtai ta kafa kwamiti biyu, daya domin wayar da kan mutane game da cutar dayan kuma domin basu tallafi
3 – Mun wadata wuraren da aka kebe domin kula da wadanda suka kamu da cutar a jihar. Mun samar da kadajen marasa lafiya akalla 100, na’aurar shakar iska, na’urar yin gwajin jutar da takunkumin fuska.
4 – kun yi wa kasuwanni feshin magani, makarantu da cikin gari baki daya.
5 – Ko a loacin da ake ta kokarin maidsa Almajirai jihohin su na asali, na mu da aka dawo da su sai da muka yi musu gwaji kafin suka shigo cikin gari.