Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 575 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –123, FCT 100, Delta 58, Edo 52, Ogun 42, Katsina 24, Bayelsa 23, Rivers 22, Borno 19, Filato18, Ondo 18, Oyo 17, Kwara 15, Osun 13, Enugu 9, Nasarawa 7, Abia 6, Cross River 5, Kaduna 3 da Ekiti 1.
Yanzu mutum 29286 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 11828 sun warke, 654 sun rasu. Zuwa yanzu mutum 16,804 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum,11,367 cases, followed by FCT – 2,281, Oyo – 1,530, Edo – 1,435, Kano – 1,268, Delta – 1,285, Rivers – 1,205, Ogun – 1,047, Kaduna – 865, Katsina 682, Borno – 547, Bauchi – 516, Gombe – 520, Ebonyi – 503, Filato – 454, Ondo – 474, Abia – 391, Enugu – 381, Imo – 352, Jigawa – 318, Kwara – 284, Bayelsa – 245, Nasarawa – 232, Osun – 175, Sokoto – 153, Niger – 122, Akwa Ibom – 112, Benue – 97, Adamawa – 99, Kebbi – 84, Zamfara – 76, Anambra – 73, Yobe – 61, Ekiti – 45, Taraba – 22, Kogi – 5 da Cross Rivers – 5.
Wasu abinci da ke kara karfin garmuwar jiki
Wasu kwararrun likitoci daga kasar UK sun shaida cewa sinadarin ‘Vitamin D’ baya warkar da cutar coronavirus.
Likitoci sun fadi haka ne ganin yadda wasu mutane ke fadin cewa sinadarin ‘Vitamin D’ na da ingancin warkar da cutar coronavirus.
Sinadarin ‘Vitamin D’ na kara karfin kashi, inganta karfin garkuwan jiki sannan yana kare mutum daga kamuwa da cututtukan dake sa a samu matsalar toshewar numfashi, kuma wara na da wannan sanadari.
A dalilin haka likitoci ke Kira ga mutane da su rika cin abinci dake dauke da sinadarin ‘Vitamin D’ domin inganta garkuwar jikinsu amma ba domin su kare kansu daga kamuwa da cutar coronavirus ba.
Abincin dake dauke da sinadarin Vitamin D sun hada da:
1. Dafaffen kwai
2. Lemun Zaki
3. Hanta dafaffe ko Kuma soyayye
4. Kifi
5. Madara
6. Madaran waken soya
7. Wara
8. Kubewa