Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 576 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum –88, Kwara-87, FCT-82, Filato-62, Ondo-39, Enugu-28, Oyo-26, Taraba-24, Kaduna-20, Ebonyi-20, Edo-17, Cross River-16, Kano-14, Rivers-11, Ogun-10, Delta-9, Nasarawa-8, Osun-8, Katsina-3, Imo-2, Kebbi-1 da Borno-1.
Yanzu mutum 37,801 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 15,677 sun warke, 805 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 21,319 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 13,626 FCT – 3,211, Oyo – 2,219, Edo – 2,017, Delta – 1,435, Rivers – 1,546, Kano –1,430, Ogun – 1,184, Kaduna – 1,211, Katsina –713, Ondo – 964 , Borno –603, Gombe – 558, Bauchi – 531, Ebonyi – 699, Filato – 762, Enugu – 705, Abia – 526, Imo – 454, Jigawa – 322, Kwara – 672, Bayelsa – 322, Nasarawa – 289, Osun – 359, Sokoto – 153, Niger – 166, Akwa Ibom – 175, Benue – 294, Adamawa – 115, Anambra – 132, Kebbi – 90, Zamfara – 77, Yobe – 64, Ekiti – 86, Taraba- 54, Kogi – 5, da Cross Rivers – 29
Matakan da Zamfara ta dauka wajen dakile yaduwar Korona a jihar.
Kakakin gwamnan jihar, Zailani Bappa ya bayyana matakan da gwamnatin jihar ta dauka da ya sa aka samu nasarar dakile yaduwar cutar a jihar.
1 – Gwamnati Zamfara ta bi dokar gwamnatin tarayya sauda kafa tun da farkon bullowar cutar a kasar nan.
Mun rufe makarantun mu tunda wuri, mun rufe kasuwanni da iyakokin jihar mu, sannan mun saka dokar kowa ya saka takunkumin fuska dole-dole. Mun yi haka ne tun kadin cutar ta dira jihar mu ma.
2 – Kafin cutar ta bulla a Zamfara gwamtai ta kafa kwamiti biyu, daya domin wayar da kan mutane game da cutar dayan kuma domin basu tallafi
3 – Mun wadata wuraren da aka kebe domin kula da wadanda suka kamu da cutar a jihar. Mun samar da kadajen marasa lafiya akalla 100, na’aurar shakar iska, na’urar yin gwajin jutar da takunkumin fuska.
4 – kun yi wa kasuwanni feshin magani, makarantu da cikin gari baki daya.
5 – Ko a loacin da ake ta kokarin maidsa Almajirai jihohin su na asali, na mu da aka dawo da su sai da muka yi musu gwaji kafin suka shigo cikin gari.