KISA: Kotu ta daure Surajo da ya caka wa makwabcin sa, Gambo, kwalba a wuya

0

Kotun ta tsare wani mazaunin rukunin gidaje na Kofar Ruwa dake Kano, Surajo Mohammed bisa kashe makwabcinsa Gambo Umar da yayi da kwalba a dalilin sabani da suka samu.

Ki da Surajo ya fusata sai ya caka wa Gambo kwalba a wuya a lokacin suna cacan baki.

Lauyan da ya shigar da karan Badamasi Gawuna ya bayyana cewa Mohammed mai shekaru 24 ya caka wa Umar makwabcin sa fasashen kwalba a wuya a dalilin rashin jituwa da ya auku a tsakanin su.

Gawuna ya ce wannan abin tashin hankalin ya auku ne ranar 7 ga watan Mayu da misalin karfe 4 na yamma a kwatas din Kofar Ruwa.

Ya ce an Kai Umar asibitin Murtala Muhammad dake Kano, sai dai kafin akai ga yi masa aiki yayi sallama da duniya.

Sai dai kuma Surajo ya musanta aikata haka a kotu, bayan sauraren zargi da ake yi masa.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 31 ga watan Agusta.

Share.

game da Author