Kwamandan Sojojin ‘Operation Safe Haven, Chukwuemeka Okonkwo, ya bayyana cewa kashe-kashen da ke faruwa a Kudancin Kaduna, wasu mabarnatan Fulani ne da mabarnatan kabilun yankin ke kashe-kashen a junan su, amma ba kisan-kare-dangi ba ne a ke yi yankin, kamar yadda wasu ke ikirari.
Manjo Janar Okonkwo ya yi wa manema labarai wannan bayani bayan fitowar su wani taron musamman kan matsalar tsaro a Kudancin Kaduna.
Ya ce, “abin da ke faruwa shi ne idan an kai hari a wannan karkara, su ma sai su kai hari a waccan karkara.”
Ya ce, “maganar gaskiya kowane bangare na kai hari a kan wani bangare, to amma ba a jin rahoton barnar da ake yi wa wani bangare. Watakila kuma yawancin gidajen jaridun ba su san cewa ana kashe kowane bangaren kabilun da ke rikicin ba.”
“Ka ga dai akwai tantiran matasan Katafawa ‘yan-sara-suka. Sannan akwai Fulani mahara da kuma wasu ‘yan iskan gari a kowane bangare.
“Sannan kuma wasu mutane na amfani da matsalar tsaron nan su na tsaro su na kai wa jama’a hare-hare.
“A yankin ana zaman gaba da kullatar juna tsakanin kabilun yankin da Fulani. Abu kadan zai tashi sai su fara kai wa juna farmaki. To kuma akwai matsalar satar shanun Fulanji.”
Daga nan ya yi alkawarin cewa sojoji a nasu bangaren za su kara kaimin kare jama’a da kyau. Ya ce sai sake sabon tsari, sabon salo da kuma sabuwar dabara.
“Idan kun san Kudancin Kaduna sosai, za ku gane cewa akwai surkukin jeji sannan kauyuka da garuriwan yankin sun yi nesa da juna. Da yawan surkukin kuwa mota ba ta iya bi. Mu na da karancin sojoji, Amma dai kun duk da haka kun dai san za mu iya yin dukkan wani kokarin da za mu iya yi.”
Daga nan ya yi albashin kara zaratan sojoji a yakin, kuma ya yi kira ga shugabannin al’ummar kabilun yankin da sauran mazauna baki daya su kauce wa dabi’ar kashe-kashe da hare-hare, su rungumi juna su zauna lafiya da juna.
A nasa jawabin, Gwamna Nasiru El-Rufai ya jaddada cewa Gwamnatin Jihar Kaduna za ta yi dukkan kokarin da ta ke kan yi domin tabbatar da zaman lafiya a Kudancin Kaduna.
Ya ce gwamnai sa ta amsa kiraye-kirayen da aka shafe shekaru goma ana yi a yankin, inda aka kafa barikin sojoji da kuma sayen wani rukunin gidaje da za a yi mazaunin dindindin na ‘yan sandan mobal. Sannan kuma an tura zaratan sojojin ‘Operation Safe Haven’ a yankin.
Sai dai kuma El-Rufai ya ce babban kandagarkin da zai wanzar da zaman lafiya a Kudancin Kaduna, shi ne kabilun da ke yankin su yi amanna da juna su zauna lafiya a tsakanin su, su daina kashe-kashen juna.
A karshe ya yi magana kan matsayar da ake ciki dangane da kwamitin binciken rigingimun can baya. Ya kuma ce duk wani mai tayar da fitina ko a wane bangare ya ke, za a kama shi a hukunta.