KARYA DOKAR KORONA: Gwamnatin Kaduna ta garkame manyan Kantina, Otel da gidajen cin abinci

0

A dalilin karya dokar Korona da wasu manyan Kantina, Otel da gidajen cin abinci da suka yi a Kaduna, gwamnatin jihar karkashin jagorancin Kwamishinan kasuwanci na jihar Idris Nyam.

An rufe gidan cin abinci na Shagalinku dake titin Ali Akilu, Cake House dake Sabon Tasha babban shagon saida abinci da buredi, Big Treat, 7 Stars Restaurant, da fitaccen gidan saida abinci na Baraka, da Naji Nice duk a hanyar Isa Kaita.

Sannan da kuma Otel din Top Galaxy, (pool/bar), Sabon Tasha da Epitome Hotel (Bar/pool) a Barnawa.

Wadannan dai manyan wuraren kasuwanci ne a Kaduna da suka yi suna da fice.

A karshe gwamnati ta yi gargadi ga masu wuraren kasuwanci da su tabbata sun bi dokokin da gwamnati ta saka don dakile yaduwar Korona a jihar.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda mutane a jihar Kaduna ke bijire wa sharuddan gujewa kamuwa da cutar covid-19 duk da cutar ke yaduwa Kamar wutan dare.

A yanzu dai mutum 1,289 be ke dauke da cutar a jihar inda hakan ya da jihar ta Zama ta 8 a jerin jihohin kasar nan da cutar ta Yi wa katutu.

Mutum dari Biyu Da Casain Da Bakwai na kwance a asibiti, an sallami 980 sannan mutum 12 sun mutu.

Share.

game da Author