KARYA DOKA: Gwamna Fintiri ya yi fatali da dokar lafiya a filin jirgin Fatakwal – Hukumar FAAN

0

Hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya, FAAN ta koka kan yadda gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya yi fatali da dokar lafiya da gwamnatin tarayya ta saka a filayen jiragen saman Najeriya, a Fatakwal.

FAAN ta koka kan yadda gwamnoni da ya kamata sune za su rika bin doka a matsayin su na shugabanni amma kuma akasin haka ake gani daga gare su.

” Ko da jirgin gwamna Fintiri ya dira filin Fatakwal, jami’an lafiya sun nemi ya dakata a gwada yanayin jikin sa da na’ura sannan ya goga man tsaftace hannaye, amma kuma ya kama ga ban sa ko sauraran su bai yi ba tare da duka tawagar sa.

” Haka kuma wadanda suka taho daga Fatakwal domin daukar sa, haka suka kutsa cikin mutane ba tare da sun kiyaye, ko kuma bi dokar lafiya ba. Daganan sai suka kama gaban su.

FAAN ta koka kan yadda jami’an gwamnati ke saba dokar gwamnatin tarayya, tana mai koka wa cewa irin haka zai sake dulmiya mutane ne cikin mummunar hadari ganin yadda ake ci gaba da samun dinbim mutanen da suke kamuwa da cutar Korona a Najeriya.

Yadda Yari ya bangaje jami’in lafiya a filin jirgin Aminu Kano

“Baka san ni shafaffe da mai bane, za ka wani ce in bi dokar lafiya” daga nan sai tsohon gwamna AbdulAziz Yari ya bangaje wannan jami’in lafiya yayi tafiyar sa.

Hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa ta koka kan yadda tsohon gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya nemi aikata dabanci a filin jirgin saman Aminu Kano kawai don jami’in lafiya ya umarce shi da ya bi dokar lafiya da aka saka a filayen jirgin.

FAAN ta shaida cewa tsohon gwamna Yari ya ki bin dokokin da aka saka a tashohin filin jiragen saman Najeriya na dakile yaduwar Korona, kamar yadda kowa yake bi.

” Irin abinda Yari yayi bai dace da wani shugaba ba, musamman ganin sune ya kamata ace ana koyi da su ba su rika karya doka ba yadda suke so kuma su nuna ba a isa a ce musu komai,

Hukumar ta kara da cewa, ” jami’in ta ya umarce shi ne da ya dan dakata ayi wa jakar sa feshi kamar yadda aka saba yi wa kowa da kowa kafin ya shiga jirgi. ” juyawar sa ke da wuya sai ya bangji jami’in ya ce ba za ayi masa b, daga nan sai ya kama gabn sa kawai yayi tafiyar sa.

Share.

game da Author