KARIN FARASHIN FETUR: Kungiyar Kwadago ta gargadi gwamnati ta koma wa tsohon farashi

0

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), ta yi fatali da karin farashin litar man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi a ranar Laraba.

Kungiyar ta bakin Shugaban ya Ayuba Wabba, ta gargadi gwamnati ta gaggauta komawa kan tsohon farashi na naira 121.50.

Kungiyar ta na magana ne kan karin kudin fetur zuwa naira 140.80 da naira 143.80.

Karin Farashin Haramtacce Ne:

NLC ta ce ta yi hanzarin neman a janye karin bisa ji da ganin yadda ‘yan Najeriya ke ta korafe-korafen karin da aka yi din.

Wata kungiya mai suna CTA, ta nami gwamnati ta bayar da cikakken bayanin dalilin karin, domin a guji yi wa talakawa karfa-karfa.

CTA ta ce samar da cikakken bayanan karin domin a fahimci yadda dokar kasa ta bayar hurumin yin karin ko kuwa ba ta bayar ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin cewa Najeriya ta kara farashin fetur a lokacin Coronavirus, tare da karin bayanin dalilin da Gwamnatin Tarayya a bayar.

Murna ta koma ciki ga ‘yan Najeriya, yayin da Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar karin farashin litar man fetur zuwa
Naira 140 har ya dangana da naira 143.

Hukumar Tantance Farashin Man Fetur (DPPRA) ce ta bayyana haka ranar Laraba din nan a Abuja.
DPPRA ta ce haka za a sha kowace litaran fetur naira 140.80k zuwa naira 143.80k cikin watan Yuli.

An yi wannan kari ne bayan a baya ana murna cewa an samu ragi zuwa naira 120 zuwa naira 123.

Karin ya zo wa ‘yan Najeriya cikin bazata, ganin yadda ake zaman kuncin tabarbarewar al’amurra dalilin barkewar cutar Coronavirus.

Cikin watan Yuni dai an sayi litar man fetur naira 121.50 zuwa 123.50.

“An yi tunanin yin wannan karin farashin ne bayan an yi nazarin yadda reshen sabat-ta-juyat-tar kasuwa ya nemi yujewa da mujiya, sakamakon maida farashin naira 121.50 da 123.50 a cikin watan Yuni.

“Jama’a a rungumi kaddarar yadda kasuwa ta nuna gejin yadda za a iya sayar da litar man fetur din. Saboda karin ya faru ne domin cike ginin kudaden ladar dako, ladar saukale daga jiragen ruwa a bakin tekun tashoshin jiragen mu. Sai kuma ladar biyan kudin dakon jigilar man daga cikin jiragen ruwa zuwa rumbunan ajiyar da gwamnati ke adana su.

Sanarwar ta ce an amimce kowane mai gidan mai ya sayar daidai gwargwadon yadda tsadar man ta kai masa shi har garin da yake sayar da man. Wato daga naira 140.80 zuwa naira 143.80.

Share.

game da Author